An Gwabza Fada tsakanin Sojoji da Barayi a Filato, an Kwato Shanu Sama da 1,000

An Gwabza Fada tsakanin Sojoji da Barayi a Filato, an Kwato Shanu Sama da 1,000

  • Dakarun Operation Safe Haven sun yi nasarar kwato shanu fiye da 1,000 da aka sace, tare da kashe ‘yan bindiga biyu a wani arangama da suka yi da su
  • ‘Yan bindigar da suka haura 60, dauke da bindigogi da suka hau babura 30, sun kutsa daga Filato zuwa wani kauyen Fulani a Taraba domin satar dabbobi
  • Sojoji daga sansanonin Jebjeb da Jihar Taraba sun hada karfi da karfe inda suka dakile harin tare da kwato dabbobin da suka hada da shanu fiye da 1,000

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Rahotanni sun bayyana cewa dakarun rundunar Operation Safe Haven (OPSH) sun yi nasarar halaka wasu ‘yan bindiga biyu da kuma kwato shanu fiye da 1,000 da aka sace.

Rahotanni sun nuna cewa an gwabza fada tsakanin sojoji da 'yan bindigar ne a kan iyakar jihohin Taraba da Filato.

Sojoji
Sojoji sun kwato shanun da aka sace a Filato. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka yi fadan ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya fara ne bayan rahoton gaggawa da sojojin suka samu a ranar 25 ga Afrilu cewa wasu ‘yan bindiga fiye da 60 dauke da makamai sun shiga jihar Taraba daga Filato.

Dakarun sojojin Najeriya sun tashi da gaggawa zuwa wurin da abin ya faru, inda suka hada kai da dakarun da ke Jebjeb a Filato suka kuma shiga sahun farautar ‘yan bindigar.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Filato

Rahoton ya ce bayan da dakarun suka hada karfi da na Jebjeb, sun bi sawun ‘yan bindigar har zuwa kauyen Komodoro da ke cikin Taraba.

Sai dai daga bisani sojojin Najeriya sun zarce da bin su har cikin dajin Daji Madam da ke jihar Filato.

A nan ne aka yi artabu da su, lamarin da ya yi sanadiyyar halaka ‘yan bindiga biyu da kuma kwato shanu fiye da 1,000 da aka sace wa Fulani.

Sojoji
Sojoji sun hallaka barayin shanu a Filato. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sojojin sun bayyana cewa an yi kofar rago ga sauran ‘yan bindigar da suka tsere kuma ana ci gaba da farautar su a dajin.

Sojoji sun kwato dabbobi fiye da 1,000

Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa dabbobin da aka kwato sun riga sun iso Jebjeb inda ake shirin mayar da su hannun masu su ba tare da bata lokaci ba.

Ya kara da cewa wannan samame na cikin dabarun rundunar na dakile hare-hare da kuma yaki da satar dabbobi a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Hukumomi sun yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri domin kawar da barazanar tsaro a yankunan su.

An kashe shanu 100 a harin Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane dauke da bindiga sun kai hari kan fulani makiyaya a jihar Filato.

Rahoto ya nuna cewa an kashe wani makiyayi daya, aka raunata da dama tare da hallaka shanu sama da 100.

Gwamnatin Filato ta ce za ta yi cikakken bincike domin gano abin da ya faru, kuma za a dauki matakin da ya dace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng