Sabon Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke A Kebbi, An Rasa Rayuka fiye da 5
- Wani sabon rikicin makiyaya da manoma da ya barke a jihar Kebbi a ranar Litinin ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane takwas
- ‘Yan sandan jihar Kebbi sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana cewa an ceto mutane biyar sannan an tura karin jami’an tsaro
- Gwamnatin Kebbi ta sanya dokar hana fita bayan afkuwar tashin hankalin domin dawo da zaman lafiya da dakile sake barkewar rikici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kebbi - Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane takwas sakamakon wani mummunan rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin makiyaya da manoman ya barke ne a garin Gulma da ke karamar hukumar Argungu a jihar ta Kebbi.

Source: Getty Images
Rikicin makiyaya da manoma a Kebbi
Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Talata, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ya ce wadanda suka mutu sun hada da manomi daya da makiyaya bakwai, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar kubutar da mutane biyar, ciki har da wata mata, a lokacin rikicin.
Usman ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana, a ranar Litinin, lokacin da aka zargi wani makiyayi mai suna Yaron Buba-Dogo da barin shanunsa suka shiga gonar wani Alhaji Aminu Ala tare da lalata amfanin gonar.
Ya ce hakan ya haifar da arangama tsakanin mutanen biyu, inda ake zargin makiyayin ya soka wa manomin wuka a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.
A cewar kakakin ‘yan sandan, mutuwar manomin ta fusata wasu mazauna yankin, inda suka taru suka kai hari kan makiyayin tare da kashe shi da kuma kona gawarsa.
An kai karin hare-hare
Mai magana da yawun 'yan sandan ya kara da cewa bayan wannan lamarin, wasu fusatattun jama’a sun ci gaba da kai hare-hare kan wasu mutanen da ke cikin garuruwan makiyayan.
“Duk da kokarin jami’an tsaro na dawo da zaman lafiya, an kashe wasu mutane hudu tare da kona gawarwakinsu har ba a iya gane su. Daga baya an gano wasu gawarwaki biyu a wata gona da ke wajen garin Gulma,."
- SP Bashir Usman.
Usman ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da mutane biyar da suka makale a lokacin rikicin tare da kai su hedikwatar ‘yan sanda ta Argungu domin kare lafiyarsu, in ji rahoton Punch.

Source: Original
An dauki matakan kawo zaman lafiya
Rundunar ta ce an tura jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro zuwa yankin domin hana sake barkewar tashin hankali.
Haka kuma gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a yankin da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya da dakile sake faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ya ce sannu a hankali zaman lafiya na dawowa, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da sintiri da sa ido a yankin.
Fadan makiyaya da manoma ya barke a Yobe
A wani labari, mun ruwaito cewa, rikici ya barke a Yobe tsakanin manoma da makiyaya bayan wani bafullatani ya shigar da dabbobinsa cikin wata gona, suka yi barna.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto mutanen da aka gani a bidiyo tare da Janar Rabe a hannun 'yan bindiga
An harbi Babayo Maina da kibiya a goshinsa, sannan aka kashe Usman Mohammed, dan shekara 35, daga kauyen Chikuriwa a rikicin da ya barke.
Jami'an tsaro sun kwato shanu da awaki da raguna, sannan suka kira shugabannin manoma da makiyaya domin warware rikicin cikin zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


