Jos
Rahotannin da muka samu yanzu haka sun nuna cewa wani abin fashewa da ake zargin bom ne ya tashi da mutane a kusa da wata kasuwa a Jos, babban birnin Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'adda sun kwashi kashinsu a kauyen Kinashe, gundumar Bashar da ke jihar Filto yayin da sojoji suka kashe Kachalla Saleh.
Hukumar kiyaye haɗurra FRSC ta ƙasa rashen jihar Filato ta tabbatar da mutuwar baki ɗaya fasinjojin wata mota da ta gamu da hatsari a Hwan Kibo yau Talata.
'Yan wasan Kano Pillars (U-19) sun yi hatsarin mota a kan hanyarsu ta zuwa sabon filin wasanni na Jos. An ce direban motar da 'yan wasa da dama sun jikkata.
Yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Filato inda suka kashe mutane biyar ciki har da wani dattijo. Yan bindigar sun yi kawanya a kauyen ne cikin dare.
Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana yadda wasu miyagun mutane su ka kai wa Fulani makiyaya farmaki a Filato tare da ankashe mutum biyu da harbe shanu.
A wannan labarin, za ku ji cewa masu kada kuri’a a jihar Filato sun bayyana rashin dadinsu kan yadda zaben kananan hukumomi ke gudana saboda rashin jami'ai.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya umarci wani basarake ya sauka daga mukaminsa domin gudanar da bincike wanda wata kungiya ta kalubanci matakin.
Babban malamin addinin Musulunci a jihar Filato ya rasu. Sheikh Zakariyya Adam Alhassan Jos ya kasance mai shiga kauyukan Fulani a Arewa domin yin wa'azi.
Jos
Samu kari