Sheikh Jingir Ya Ballo Aiki, Lauya Ya Dura Kansa Saboda Tallar Muslim Muslim

Sheikh Jingir Ya Ballo Aiki, Lauya Ya Dura Kansa Saboda Tallar Muslim Muslim

  • Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya ce kalaman Sheikh Yahya Jingir na iya ƙara rura rikicin addini a Najeriya
  • Adeyanju ya yi kira ga malaman addini da su yi amfani da tasirinsu wajen inganta zaman lafiya da haɗin kan ƙasa
  • Sheikh Sani Yahaya Jingir ya sake bayyana goyon bayansa ga tikitin Musulmi-Musulmi gabanin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Lauyan kare hakkin ɗan Adam, Deji Adeyanju, ya yi Allah-wadai da kalaman da malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Jingir, ya yi na goyon bayan ci gaba da amfani da tikitin Musulmi-Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa.

Deji Adeyanju ya yi gargadin cewa kalaman addini da za su iya ƙara kawo rarrabuwar kawuna da za su iya barazana ga haɗin kan Najeriya.

Deji Adeyanju ya soki Sheikh Jingir
Lauya Deji Adeyanju da Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: Adeyanju Deji
Source: Facebook

Adeyanju, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2026 a shafinsa na Facebook, ya bayyana kalaman Jingir a matsayin masu rarrabuwar kawuna da kuma waɗanda za su iya ƙara rura rikicin addini a ƙasar.

Kara karanta wannan

Rigima ta yi zafi, Atiku ya yi tone tone kan Obasanjo

Adeyanyu ya yi martani ga Sheikh Jingir

Adeyanju ya ce Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai, kuma Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya amince da wannan bambancin addini tare da kare shi.

Ya yi kira ga shugabannin addini da su mutunta wannan bambancin tare da amfani da tasirinsu wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai maimakon haifar da saɓani tsakanin Kiristoci da Musulmai.

Adeyanju ya yi Allah wadai da kalaman Jingir

“Na yi Allah-wadai da kalaman baya-bayan nan na Sheikh Yahya Jingir a matsayin kalaman da ke rarrabuwar kawuna kuma za su iya rura rikicin addini. Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai, kuma Kundin Tsarin Mulkinmu ya amince da wannan bambancin tare da kare shi."
"Ya kamata shugabannin addini su mutunta bambancin Najeriya tare da amfani da tasirinsu wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai maimakon haifar da rashin jituwa tsakanin Kiristoci da Musulmai."
“Shin tikitin Musulmi-Musulmi ya sanya abinci a kan teburin ’yan Najeriya, ya magance matsalar rashin tsaro, rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki, ko ya ƙarfafa fasfo ɗin Najeriya da martabar ƙasar a duniya? Dole ne mu kalli abin da ya wuce addini, mu auna shugabanci bisa tasirinsa ga rayuwarmu a matsayin ’yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Najeriya na iya rasa tallafin Amurka na dala biliyan 1.4, an gano babban dalili

“Duk wani kalami da ke hada fada tsakanin wata ƙungiyar addini da wata, kalami ne da zai ƙara zurfafa rarrabuwar kanmu tare da rura tashin hankali a sassan ƙasar. Malaman addini da ’yan siyasa su daina tsokanar ’yan ƙasa masu bin doka, su kuma koyi mutunta addinai, al’adu da ƙabilunmu daban-daban. Najeriya tamu ce baki ɗaya.”

- Deji Adeyanju

Adeyanju ya soki Sheikh Jingir
Deji Adeyanju na jawabi a wajen taro Hoto: Adeyanju Deji
Source: Twitter

Fasto ya taro rigima da Sheikh Jingir

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani malamin addinin Kirista ta fito yana sukar Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir kan yadda APC ta tsayar da Musulmi takara a Plateau.

Faston ya bayyana cewa ba za su yarda a ba mai sallah damar yin takara a jihar ba, yana danganta lamarin da kokarin sayar musu da kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng