Almajiranci ba ya amfanar Almajirai, ba ya amfanar Najeriya inji El-Rufai

Almajiranci ba ya amfanar Almajirai, ba ya amfanar Najeriya inji El-Rufai

- Gwamnan Kaduna ya ce za su yi kokari wajen kashe karatun Almajiranci

- Malam Nasir El-Rufai ya ce irin wannan tsarin karatu bai da wani amfani

- Musulmi sun dade su na neman ilmin addini da tsarin Almajiranci a Arewa

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi magana game da tsarin karatun almajiranci, inda ya kushe shirin, ya ke cewa dole a dakatar da shi domin ba ya aiki a kasar.

Nasir El-Rufai ya yi hira da gidan jaridar Channels TV a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, 2020, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta maida almajirai 30, 000 inda su ka fito.

Mai girma gwamnan ya kuma tabbatar da cewa a shirye jihar Kaduna ta ke ta karbi ‘ya ‘yanta da su ke almajiranci a wasu jihohin kamar yadda wasu su ke dawowa daga Kano.

Gwamnan ya ke cewa sun dade su na neman hanyar kawo karshen tsarin karatun da ake yi, sai a yanzu ne annobar cutar COVID-19 ta bada damar gano inda almajiran su ke.

KU KARANTA: An sake samun wasu Almajirai 16 da ke da cutar COVID-19

Malam El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta Kaduna ta fara aiki a kan dokar da za ta haramta tsarin. Idan wannan doka ta samu shiga, babu mahaifin da zai tura yaronsa almajiranci.

Gwamna El-Rufai ya ke cewa: “Ya zama dole a daina tsarin almajiranci saboda shirin bai yi wa yaran aiki ba, bai yi wa arewacin Najeriya aiki ba, kuma bai yi wa Najeriya aiki ba.”

El-Rufai ya shaidawa jaridar cewa jihohin Arewa karkashin shugabancin gwamnan Filato, Simon Lalong sun dauki tsawon lokaci su na duba hanyar da za a bi wajen tsaida tsarin.

Gwamnan ya koka da yadda ake barin yara su na yawon bara da sunan karatu, ya ce jihohi za su yi bakin kokari wajen ganin an kashe almajiranci. “Kowane tsari ya fi wannan."

Almajirai fiye da 50 da su ka dawo daga jihar Kano aka samu dauke da cutar COVID-19 a Kaduna. A cewar gwamnan, da an yi sake da wasu daga cikin almajirai sun mutu a Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel