EFCC Ta Rufe Asusun Gwamnatin Jiha Sukutum, An Jefa Gwamna a Matsala dab da Zabe

EFCC Ta Rufe Asusun Gwamnatin Jiha Sukutum, An Jefa Gwamna a Matsala dab da Zabe

  • Hukumar EFCC ta rufe wani asusun gwamnatin Osun wanda ake amfani da shi wajen biyan albashin ma'aikata kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna
  • Gwamna Ademola Adeleke ya ce tun da farko ya yi gargaɗin cewa ana shirin daskarar da asusun gwamnati domin kawo cikas ga ayyukan gwamnati
  • Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ba a bayyana dalilin da ya sa aka ɗauki matakin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Osun - Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta daskarar da wani asusun gwamnatin jihar Osun da ke ajiye a First Bank, kwanaki 10 kafin gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Rahotanni sun ce asusun da aka sanya masa dokar "Post No Debit" na daga cikin waɗanda gwamnatin jihar ke amfani da su wajen biyan albashin ma'aikata.

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun
Jami'an hukumar EFCC a bakin aiki (hagu) da Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke. Hoto: @officialEFCC, @AAdeleke_01
Source: Facebook

Adeleke ya yi zargin shirin EFCC

Matakin na EFCC ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi zargin cewa hukumar na shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da na wasu manyan jami'an gwamnati.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na jihar, Kolapo Alimi, ya fitar a ranar Laraba, wanda aka wallafa a shafin gwamnatin Osun na X.

A sanarwar, gwamnan ya ce hakan wani yunƙuri ne na kawo cikas ga ayyukan gwamnati gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta.

Adeleke ya kuma yi iƙirarin cewa babu wata hujja ta doka da ta bai wa EFCC ikon daskarar da asusun gwamnatin jiha, yana mai cewa hukumar ba ta da hurumin ɗaukar irin wannan mataki kamar yadda muka ruwaito.

An rufe asusun gwamnatin Osun

Wata majiya da ke kusa da gwamnan, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana a hukumance, ta tabbatar da cewa an riga an daskarar da asusun.

Kara karanta wannan

Adeleke ya zargi EFCC da shirin yi wa gwamnatinsa illa gabanin zaɓen Osun

Majiyar ta ce yanzu lamarin ya wuce zargi, domin asusun ya daina aiki bayan matakin da EFCC ta ɗauka.

Ta ƙara da cewa ana sa ran gwamna Ademola Adeleke zai yi wa manema labarai jawabi domin ƙarin haske kan halin da ake ciki, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Tuni dama gwamna Adeleke ya yi zargin cewa EFCC a ta rufe asusun gwamnatin jihar.
Gwamnan Osun Ademola Adeleke da EFCC ta rufe wa asusun gwamnatin jiha. Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

EFCC ba ta yi magana ba

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Hukumar EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun ba.

Haka kuma, ba a bayyana dalilin da ya sa aka sanya takunkumin kan asusun ba, yayin da ake ci gaba da jiran karin bayani daga hukumar.

Adeleke ya gargadi EFCC

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Ademola Adeleke, ya gargaɗi shugaba Bola Tinubu da kada ya bari a tafka maguɗin zaɓen gwamnan Osun da za a yi ranar 15 ga Agusta.

Adeleke ya ce duk wani yunƙurin maguɗin zaɓe na iya janyo rikicin siyasa irin wanda ya faru a shekarar 1983, yana mai cewa al'ummar Osun ba za su amince da hakan ba.

Gwamnan ya kuma buƙaci Tinubu ya dakatar da abin da ya kira cin zarafin 'yan siyasa da jami'an 'yan sanda ke yi, tare da umartar shugabannin APC su guji tayar da tarzoma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com