NLC
An tabbatar da rasuwar babban sakataren kungiyar kwadsgo ta Najeriya, NLC, Emmanuel Ugboaja yana da shekaru 60 a duniya, ya rasu bayan doguwar jinya.
Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya ce albashinsa N503,000 ne, yayin da manyan sakatarorin gwamnati ke samun N900,000, wasu kuma har N1m suke samu.
Zanga-zangar NLC ta dakatar da zirga-zirgar jirage a Legas, inda fasinjojin Air Peace suka makale yayin da ake bukatar ma’aikatan kamfanin su shiga kungiyar kwadago
A labarin nan, za a ji cewa bakin NLC, TUC da kungiyoyin ya zo daya game da albashin N70,000 da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince a ba ma'aikata.
Kungiyoyin NLC da TUC sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa N500,000, yayin da wa’adin karin N70,000 ya kare a watan Yuli.
Kungiyar ma'aikata ta JNPSNC ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi wa ma'aikata karin albashi da kashi 40 saboda N70,000 ba ta wadatar da su.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar Taraba ta rage albashin masu share tituna daga N15,000 zuwa N10,000. An ce wanda ba zai iya ba ya ajiye aikin.
Kungiyoyin NLC da TUC sun sanar da shirin fara tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi, saboda hauhawar farashi da ta yi wa ma’aikata katutu.
Kungiyar NLC ta tabbatar da rasuwar shugaban JNC na jihar Legas, Domingo Michael Adaeleke a taron kwadago na duniya da ke gudana a birnin Geneva.
NLC
Samu kari