Mafi karancin albashi
Gwamna Abdullahi Sule ya tabbatar da fara biyan sabon albashin N70,500, amma jihar ba za ta iya ɗaukar karin albashin da ake buƙata ba saboda rashin kuɗi.
Yan kwadago sun fasa shiga yajin aikin da suka yi niyya bayan Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya amince da N80,000 a sabon mafi ƙarancin albashi.
Yan kwadago sun tabbatar da cewa tun a Nuwamba, 2024, ma'aikata suka fara ganin sabon mafi ƙarancin albashi, sai dai ba a aiwatar da shi yadda ya dace ba.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta dakatar da yajin aikin da ta fara kan sabon mafi karancin albashi. Ta dakatar da yajin aikin na sati daya.
Kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Neja ta yaba wa Gwamna Bago kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N80000 wanda ya fi na sauran jihohin Arewa ta Tsakiya.
Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ƴan kwadago, za a fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a watan Maris, 2025.
Ma’aikatar kudi ta jihar Kwara ta ce biyan albashi yana gudana bisa tsarin rajistar KWSRRA, ma’aikatan da ba su samu albashin Nuwamba ba basu yi rijistar ba.
'Yan kwadago sun tafi yajin aiki a Kaduna, Nasarawa, Ebonyi da Cross River saboda gaza karin sabon mafi karancin albashi. NLC ta rufe ofis ofis a jihohin.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sha alwashin cewa zai maye gurbin duk ma'aikacin da bai fita aiki ba na tsawon kwanak uku saboda yajin aikin NLC.
Mafi karancin albashi
Samu kari