Albashin ma'aikatan najeriya
Babban bankin Najeriya na CBN ya fara shirin sallamar ma'aikata kimanin 1,000 kuma zai ba su kudin ritaya sama da N50bn yayin sallamarsu kafin karshen 2024.
Kungiyar kwadago reshen jihohi akalla shida sun sanar da janyewarsu daga yajin aikin da NLC za ta shiga a jihohin da ba a fara biyan sabon mafi karancin albashi ba.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya amince a biya ma'aikatan jihar albashi na watan 13. Gwamnan ya kuma amince da daukar aiki ga wadanda suka kammala karatu.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamna Radda zai rika biyan albashin N70,000.
Gwamnatin jihar Kaduna ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N72,000 ga ma'aikatan jihar a watan Nuwamba. Gwamnati na jiran koke daga ma'aikata.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya fara biya ma'aikata mafi karancin albashin N85,000 kamar yadda ya yi alkawari a baya inda ma'aikatan suka yi godiya.
Gwamnan Imo, Hope Uzodimma ya sanar da amincewarsa na fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikatan jihar. Ya karawa wasu albashi.
Yan kwadago na barazanar tafiya yajin aiki a jihohin Katsina, Imo, Zamfara da Cross River a kan karin mafi ƙarancin albashi zuwa ranar 1 ga watan Disamba.
Gwamnatin Bauchi ta sanar da lokacin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a karshe watan Nuwamba. Bala Muhammad ya ce zai biya hakkokin ma'aikata a jihar.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari