Imo da Sauran Jihohin Najeriya da Ma'aikata Ke Karbar Albashi Mai Tsoka a 2026
- Kimanin shekaru biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar sabon albashin N70,000, jihohi da dama sun aiwatar da canjin
- Rahoto ya nuna cewa jihar Imo ce ke kan gaba wajen biyan albashi mai tsoka, inda ma'aikata ke karbar mafi karanci N104,000, sai Ebonyi da N90,000
- A yayin da aka yi bikin ranar ma'aikata ta 2026, kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana aniyarta na sake yin zama da gwamnati kan sabon albashi
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Bayanai da aka samu game da albashin ma'aikata a shekarar 2026 sun nuna cewa jihohi da dama sun jima da aiwatar da sabon tsarin albashi na ƙasa.
Yayin da doka ta tanadi N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin, wasu jihohin sun ƙara kudin domin tallafa wa ma'aikata duba da yanayin tattalin arziki.

Source: Twitter
Shafin Nairametrics ya wallafa a X yadda jerin biyan albashin yake a jihohin Najeriya daban-daban:
Albashin N70,000 zuwa N79,999
Mafi yawan jihohin Najeriya suna cikin wannan rukunin, inda suka fara daga matakin N70,000 da doka ta tanada.
- Sokoto - N70,000
- Zamfara - N70,000
- Katsina - N70,000
- Jigawa - N70,000
- Yobe - N70,000
- Borno - N70,000
- Bauchi - N70,000
- Plateau - N70,000
- Taraba - N70,000
- Adamawa - N70,000
- Kwara - N70,000
- Kogi - N70,000
- Ekiti - N70,000
- Anambra - N70,000
- Abia - N70,000
- Delta - N70,000
- Cross River - N70,000
- Kano: N71,000
- Gombe: N71,451.15
- Kaduna: N72,000
- Ondo: N73,000
- Kebbi, Benue, Edo: N75,000
- Osun: N75,554
- Ogun: N77,000
Sai dai duk da haka, wani rahoto na jaridar This Day ya nuna cewa har yanzu akwai jihohin da ba su fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba, duk da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar albashin a Yulin 2024.

Kara karanta wannan
NLC, TUC sun tsayar da lokacin tattauna sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Najeriya
Jihohin da ke biyan albashin fiye da N80,000
Wasu jihohin, musamman a kudancin Najeriya da kuma jihar Niger, sun tsallake shingen N80,000 domin ƙarfafa tattalin arzikin ma'aikatansu.
- Niger: N80,000
- Oyo: N80,000
- Enugu: N80,000
- Bayelsa: N80,000
- Akwa Ibom: N80,000
- Rivers: N85,000
- Lagos: N85,000
Wannan mataki na nuna gasa ta gari tsakanin jihohi wajen ganin wacece za ta fi karkato da hankalin ƙwararrun ma'aikata ta hanyar biyan albashi mai tsoka.
Jihohin da suka fi albashi mai tsoka

Source: Facebook
A halin yanzu, jihohi biyu ne kawai suka shiga rukunin N90,000 zuwa sama, inda suka bar sauran jihohin a baya.
- Ebonyi: N90,000
- Imo: N104,000
Jihar Imo ce ta zama zakara a faɗin Najeriya, inda take biyan kusan ninki ɗaya da rabi na abin da mafi yawan jihohi ke biya. Wannan babban ci gaba ne ga ma'aikatan jihar waɗanda ke fuskantar tsadar rayuwa.
NLC za ta tattauna sabon albashi da gwamnati
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyoyin ƙwadago da suka hada da NLC da TUC sun ce za a fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata
Wannan batu ya taso ne a lokacin da Najeriya ta yi bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a ranar Juma'a, 1 ga watan Mayu, 2026.
Ƙungiyoyin sun jaddada bukatar a hada kai, a yi magana da baƙi ɗaya idan an tashi tunkarar lamarin kara wa ma'aikatan Najeriya albashi.
Asali: Legit.ng
