Gwamnoni Sun Bukaci Tinubu Ya Dawo da Mafi Karancin Albashi N100,000

Gwamnoni Sun Bukaci Tinubu Ya Dawo da Mafi Karancin Albashi N100,000

  • Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci a kara mafi karancin albashi zuwa N100,000
  • Ya ce karin albashin zai dace da halin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu da kuma bukatar inganta jin dadin ma’aikata da magance matsalar tsadar rayuwa
  • Gwamnan ya kara da cewa gwamnatocin jihohi na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago domin cimma matsaya mai dorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Gwamnonin da ke karkashin inuwar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) sun bukaci shugaba Bola Tinubu ya yi la’akari da kara mafi karancin albashi zuwa N100,000.

Sun yi magana suna masu nuna karuwar kudin shiga da jihohi suka samu bayan cire tallafin man fetur da sauran gyare-gyaren kudi da gwamnatin ta aiwatar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda cire tallafin mai ya hana Najeriya durkushewa

Bola Tinubu da gwamnoni
Gwamnoni na tattaunawa da Bola Tinubu a Legas. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa an fada wa Tinubu bukatar ne a ranar Juma’a ta bakin shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.

Dalilin neman karin albashi

AbdulRazaq ya ce cire tallafin man fetur da gyare-gyaren kudi da suka biyo baya sun kara karfin tattalin arzikin gwamnatocin jihohi sosai, lamarin da ya ba jihohi da dama damar sauke nauyin da ke kansu tare da rage bashin da ake bin su.

“Ina ganin al’umma sun yi mamakin jajircewar shugaban kasa wajen aiwatar da wannan muhimmiyar manufa, amma a yau kasar ta amfana matuka daga wannan mataki,”

In ji gwamnan.

Ya bayyana cewa jihohi da dama da a baya suke dogaro da karbar bashi domin gudanar da ayyuka da kashe-kashen yau da kullum yanzu suna cikin yanayin kudi mafi kyau.

TVC ta rahoto gwamnan jihar Kwara ya ce:

“Jihohi da dama sun kasance suna karbar bashi. Yanzu jihohi ba za su je neman bashi ba; ba za su fitar da takardun bashi ba. Hasali ma, muna rage bashinmu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Trump zai kawo sabon kudi mai dauke da hoton shi a Amurka

"Ina rokon Mai Girma Shugaban Kasa ya bari a tattauna batun kara mafi karancin albashi zuwa akalla N100,000,”
Gwamnonin Najeriya da Bola Tinubu
Bola Tinubu tare da gwamnoni bayan ganawa a Legas. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Bayanin Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shettima, ma ya yaba da matakin cire tallafin man fetur, yana mai bayyana shi a matsayin jarumtaccen mataki da ya fuskanci matsalolin da suka dade suna nakasa tattalin arzikin kasar.

Gwamnonin jihohin Lagos, Nasarawa, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Taraba, Niger, Ekiti, Delta, Ondo, Edo, Adamawa, Benue, Enugu, Ogun da Kogi ne suka halarci taron, tare da mataimakan gwamnonin Borno da Kano.

Bayanim Tinubu kan tallafin mai

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi a 2023 ya ceci kasar daga durkushewar tattalin arziki.

Baya ga ceto Najeriya, shugaban kasa Tinubu ya ce gwamnatinsa ta shimfida tubalin farfadowar tattalin arzikin kasa da yanzu haka kowa na gani a kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin gwamnonin jihohi da suka je taya shi murnar sallah da kuma cika shekaru uku da gwamnatinsa ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng