Ana Batun 2027, Kwankwaso Ya Bude Kofar Sake Hada Tafiya da Gwamna Abba
- Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan yiwuwar sake tafiya tare da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
- Babban 'dan siyasar ya bayyana cewa ba Abba Kabir kawai ba, duk wanda ya tuba bayan fita daga tafiyar Kwankwasiyya yana maraba da shi
- Abba Kabir Yusuf ya samu kujerar gwamnan jihar Kano ne bayan Sanata Rabiu Kwankwaso ya mara masa baya a zabukan 2019 da 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sake magana kan alakar shi da Abba Kabir Yusuf da ya lashe zaben gwamnan Kano a 2023.
Kwankwaso ya bayyana cewa ba korar Abba Kabir Yusuf ya yi ba a tafiyar Kwankwasiyya, shi gwamnan ne ya tafi ba tare da izinin shi ba.

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin hira da BBC Hausa, inda tashar ta wallafa bidiyon bayanin da ya yi a shafinta na X.
'Ina son Abba,' Rabiu Kwankwaso
Da aka tambaye Rabiu Kwankwaso ko zai yaki Abba Kabir a 2027, ya ce shi ba ya yakin kowa, yana abubuwan da suka sha gaban shi ne kawai.
Ya bayyana cewa duk da haka, Abba Kabir Yusuf da kan shi ya san cewa matukar zabe za a yi na adalci, ya san ba za a iya kayar da Kwankwasiyya ba a Kano.
Dangane da watsi da Abba Kabir Yusuf, Kwankwaso ya ce shi bai kori Abba Kabir daga tafiyar Kwankwasiyya ba, ya ce shi a bar tafiyar da kanshi.
Ya ce:
"Ai ba yar da shi na yi ba, ai ni ina son shi, ai ba ni na ce ya tafi ba, ai ba korarsa muka yi ba."
Alakar Kwakwaso da Ganduje a baya
Da aka tambayi Kwankwaso ko zai iya dawowa yin alaka da Abba idan ya nemi gafarar shi a yanzu, sai ya tuna wasu abubuwa da suka faru tsakanin shi da Abdullahi Umar Ganduje.
Kwankwaso ya ce ya yi rigima da Ganduje, ba daya ba, ba biyu ba, ba uku ba a shekarun baya da suke tafiya tare a harkokin siyasa.
Ya ce:
"Ganduje sau nawa ana rigima da shi, ya kalubalance ni kashi-kashi, a 2007 ma yana SA dina ya shirya yadda za a kayar da ni."

Source: Facebook
Ya ce duk da abubuwan da Ganduje ya masa a baya ya yafe masa kuma ya mara masa baya ya zama gwamnan jihar Kano.
A karkashin haka, Kwankwaso ya bayyana cewa a shriye ya ke ya yafewa duk wani dan Kwankwasiyya da aka samu sabani da shi.
Kwankwaso na tare da Obi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu yana tare da Peter Obi a jam'iyyar adawa ta NDC.
Kwankwaso ya bayyana cewa zai yi wa Obi mataimakin shugaban kasa a NDC kuma idan Allah ya ba su nasara za su yi aiki kafada da kafada.
Ya kara da cewa an yi yarjejeniya da Obi cewa wa'adi daya zai yi a kan mulki idan ya ci zabe, daga nan kuma a dawo da mulki Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


