An Saki Sunayen Kananan Hukumomi 3 da Boko Haram Ta Tilasta wa Biyan Haraji a Yobe
- Gwamnatin Yobe ta ce za ta kara kaimi wajen dakile hare-haren Boko Haram da karbar harajin dole daga manoma a jihar
- Mataimakin gwamnan jihar ya bayyana cewa ‘yan ta'adda na tilasta wa jama’a biyan kudade a kananan hukumomi 3
- Gwamnatin Yobe ta yi ta’aziyyar jami’an tsaro da suka mutu a harin da aka kai makarantar horas da sojoji a Buni Yadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yobe - Gwamnatin Yobe ta bayyana kudirinta na kara daukar matakai domin dakile hare-haren Boko Haram da kuma hana karbar harajin dole daga manoma da mazauna wasu sassan jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde Gubana, ne ya bayyana hakan yayin taron kwamitin tsaro karo na 18 da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Damaturu ranar Laraba.

Source: Facebook
Boko Haram ta kakaba haraji a Yobe
Gubana, wanda ya wakilci Gwamna Mai Mala Buni a taron, ya ce an kira taron gaggawar ne bayan sababbin hare-haren da aka kai sansanonin sojoji a jihar, in ji rahoton Daily Trust.
Ya bayyana cewa lamarin na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da jihar ta dade tana morewa.
Mataimakin gwamnan ya nuna damuwa kan yadda ake zargin ‘yan Boko Haram na tilasta wa jama’a da manoma biyan haraji a kananan hukumomin Yunusari, Geidam da Tarmuwa.
A cewarsa:
“Kamar yadda kuka sani, an samu hare-hare kan sansanonin sojoji a kwanakin baya, sannan ana tilasta wa mutanenmu biyan haraji da tara a Yunusari, Geidam da Tarmuwa da sauran yankuna.”
'An ɗan samu zaman lafiya a Yobe'
Gubana ya ce taron zai tattauna kan sauran matsalolin tsaro da suka hada da rikicin manoma da makiyaya, fasa gidaje da sauran laifuffukan da ke kawo cikas ga zaman lafiya.
A cewar maimakin gwamnan, duk da cewa jihar ta samu dan zaman lafiya a baya-bayan nan, abubuwan da suke faru wa sun nuna bukatar kara himma wajen yaki da ta’addanci
“Mun samu dan zaman lafiya, amma da irin abubuwan da ke faruwa yanzu dole mu kara kaimi domin dakile duk wani nau’in laifi a cikin al’umma,” in ji Gubuna

Source: Original
Ta'aziyya da neman hadin kan jama'a
Gwamnatin Yobe ta kuma jajanta wa rundunar soji da ‘yan sanda bisa mutuwar jami’an tsaro a harin da aka kai makarantar horas da jami’an tsaro ta NETTS da ke a Buni Yadi, karamar hukumar Gujba.
Gubana ya ce gwamnatin jihar na mika ta’aziyya ga shugaban rundunar soji da Sufeto Janar na ‘yan sanda bisa wannan rashi in ji rahoton Punch.
A karshe, gwamnatin jihar ta bukaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
An kama mai taimaka wa Boko Haram
A wani kabari, mun ruwaito cewa, sojoji sun yi nasarar damke wani mutumi da ake zargin dan leken asirin Boko Haram ne a Yobe.
Rahoto ya nuna cewa bayan kama mutumin, sojoji sun mika shi sashen leken asiri na rundunar Operation Hadin Kai domin ci gaba da bincike.
Wannan dai na zuwa ne yayin da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP ke karuwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng

