Tsaro: Fulani da Ke Zaune a Kudancin Najeriya Tsawon Shekaru Sun Fara Tserewa
- Fulani mazauna Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma sun fara barin yankunan da suka zauna tsawon shekaru
- Shugabannin MACBAN sun ce ana kashe makiyaya marasa laifi, ana korarsu daga gidajensu, tare da danganta Fulani da ta'addanci
- Duk da damuwar al'umma kan rashin tsaro, Fulani sun ce suna haɗin gwiwa da jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Fulani da dama da suka zauna a yankunan kudancin Najeriya tsawon shekaru suna ci gaba da barin garuruwansu.
Majiyoyi sun alakanta hakan da zargin wariyar ƙabilanci da ƙaruwar rashin tsaro a yankunan da suke zaune.

Source: Twitter
Yadda Fulani ke tserewa daga Kudancin Najeriya
Binciken Punch ya nuna cewa Fulani mazauna Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma suna tserewa ko kuma ana tilasta musu barin yankunan da suka zauna tsawon lokaci.
Al'ummomin da suka karɓe su suna zargin wasu Fulani da hannu a ta'addanci da ayyukan 'yan bindiga, lamarin da ya ƙara dagula zamantakewa.
Wasu daga cikin Fulani sun bayyana cewa suna fuskantar ƙiyayya, yayin da aka sace shanunsu a wurare daban-daban da suke rayuwa.
Sun ce wannan yanayi ya sa wasu makiyaya da masu kiwon dabbobi suka fara komawa wasu ƙasashen Yammacin Afirka da wuraren da suke ganin sun fi aminci.
Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da kashe-kashe da garkuwa da mutane suka ƙaru a sassan ƙasar nan, abin da ya ƙara zarge-zarge.
Duk da damuwar mazauna yankunan da abin ya shafa kan laifukan tashin hankali, shugabannin Fulani da kungiyar Miyetti Allah sun wanke mambobinsu daga aikata laifuka.
Sun ce wariyar ƙabila ta haddasa kashe-kashe, korar mutane daga gidajensu da kuma tilasta wa makiyaya marasa laifi yin ƙaura.
Fulani sun koka a Kudu maso Yamma
Shugaban MACBAN na Kudu maso Yamma kuma Sarkin Fulani na Abeokuta, Alhaji Muhammad Labar, ya ce tsoro ya bazu tsakanin Fulani a yankin, cewar Daily Post.
Labar ya tabbatar da cewa wasu makiyaya sun bar Kudu maso Yamma tare da shanunsu zuwa wasu ƙasashe makwabta da yankunan da suke ganin sun fi aminci.
Ya ƙara da cewa MACBAN ta ƙara wayar da kan mambobinta domin hana firgici da ƙarfafa zaman lafiya da al'ummomin da suke zaune tare.
Ya ce:
"Muna gaya wa mutanenmu su kwantar da hankalinsu saboda mun san junanmu kuma mu 'yan Najeriya ne masu son zaman lafiya.
"Muna zaune a wasu daga cikin waɗannan yankuna tun kaka da kakanni, kuma muna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki ta hanyar kiwon dabbobi.
Ya ce duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukunci bisa doka, ba tare da la'akari da asalinsa ba.
Rahotanni sun kuma gano cewa makiyaya na fuskantar ƙarin tsangwama da ƙiyayya, yayin da ake zargin an kashe wasu ko aka kore su.

Source: Getty Images
Shugabannin Fulani sun koka a Enugu
Mataimakin Darakta Janar na MACBAN mai kula da Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, Gidado Siddiki, ya ce makiyaya na shan wahala.
Ya ce suna fuskantar tsangwama, ƙiyayya da korarsu daga wasu jihohin Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta hana Katsina da wasu jihohin Najeriya yin sulhu da 'yan bindiga
A madadin mutanensa, ya nuna damuwa kan tsaron makiyaya a Enugu, inda ya ce an kashe wasu daga cikinsu a wasu yankuna.
Shugaban a bayyana Enugu a matsayin mafi wahalar muhalli ga makiyaya a yankin Kudu maso Gabas.
Siddiki ya ce daga watan Nuwamban 2025 zuwa Mayun 2026, an kashe makiyaya akalla 11 a yankuna daban-daban.
A cewarsa, an kai rahoton mafi yawan waɗannan hare-hare ga jami'an tsaro amma har yanzu ba a warware su ba.
Siddiki ya kuma ce an kori Fulani daga ƙauyen Nkaleha a Ebonyi duk da sulhun da DSS ta jagoranta.
Halin da Fulani suke ciki a Abia
A Abia, wani mai suna Ali Tongo ya ce ana samun kwanciyar hankali a mafi yawan yankuna, amma ana ci gaba da nuna wariya ga wasu makiyaya.
Ya ce a Anambra an samu ci gaba wajen tsaro, duk da cewa an kashe makiyaya sama da 50 tsakanin 2021 da 2024.
Sai dai ya yaba wa matakan tsaro da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka ɗauka, wanda ya rage tashe-tashen hankula.
Amurka ta magantu kan Fulani 'yan ta'adda
Mun ba ku labarin cewa hukumar USCIRF ta ce akwai kimanin Fulani masu ɗauke da makamai 30,000 da ke kai hare-hare a Najeriya cikin ƙungiyoyi daban daban.
Rahoton ya bayyana cewa hare-haren da ake dangantawa da mayaƙan Fulani sun haddasa dubban mace-mace da raba al’umma da matsugunansu.
USCIRF ta zargi jami’an tsaro da jinkirin kai dauki yayin da kungiyar Miyetti Allah ta musanta hannu a duk wani tashin hankali da ake yi a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


