
Aikin noma a Najeriya







Gwamnatin tarayya ta ce jama'a su kwantar da hankulansu, inda ta ƙaryata cewa akwai tsoron ƙasa za ta iya faɗawa a cikin ƙarancin abinci a ƴan kwanaki masu zuwa.

Gwamnatin Neja za ta fara fitar da kayan abinci daga Arewacin Najeriya zuwa kasashen ketare. Hukumar FAAN ta ce za ta yi hadin gwiwa da jihar kan lamarin.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya fara sabon awaki ga mata da makiyaya a faɗin jihar, ya ce shirin zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kiwo.

Masu ruwa da tsaki a kasuwar kayan abinci ta Singer sun bayyana yadda saukar farashin Dala, manufofin Tinubu da kaka suka taimaka wajen saukar farashin abinci.

Gwamnan Neja Umaru Bago ya ware tirelolin abinci 1,000 domin karya farashi a Ramadan. Za a raba tirela 500 kyauta, za a sayar da tirela 500 a farashi mai rahusa.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai shiri da aka yi domin tabbatar da cewa 'yan kasar nan sun samu sauki a farashin abinci a kasuwannin kasar.

Gwamnatin jihar Jigawa ta yi hadaka da masana daga Saudiyya domin habaka noman dabino, za a mayar da Jigawa mafi yawan noma da samar da dabino a Najeriya da Afrika.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce bai kamata ƙasa kamar Najeriya mai ɗumbin aƙbarkatu ta gaza samar da wadataccen abinci da ƴan ƙasa ba.

Gwaman jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba tallafin N400m ga kungiyoyin matasan Kano domin fara sana'ar noma. Shirin na karkashin ACReSAL da bankin duniya
Aikin noma a Najeriya
Samu kari