Keyamo Ya Gano Wanda zai Ci Zaben 2027 tsakanin Tinubu, Obi da Atiku

Keyamo Ya Gano Wanda zai Ci Zaben 2027 tsakanin Tinubu, Obi da Atiku

  • Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce shugaba Bola Tinubu zai samu nasara cikin sauki a zaben shugaban kasa na 2027
  • Keyamo ya ce sakamakon lissafin karfin siyasa da yawan masu kada kuri'a ya nuna cewa zaben 2027 zai zama tamkar nadin sarauta ga Tinubu
  • Ministan ya kuma yi watsi da barazanar da Atiku Abubakar da Peter Obi za su iya yi wa APC, yana mai cewa ba ya ganin inda za su samo kuri'u

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 cikin sauki.

Keyamo ya ce bisa la'akari da yanayin siyasa da lissafin karfin kuri'u, zaben shugaban kasa mai zuwa ba zai zama takara ba, illa tamkar nadin sarauta ga Tinubu.

Kara karanta wannan

'Kuskuren da Atiku, Obi da Kwankwaso ke yi da zai ba Tinubu mulki a sauƙi'

Festus Keyamo da Bola Tinubu
Festus Keyamo a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Festus Keyamo ya bayyana haka ne yayin wata hira da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis.

Batun nasarar Tinubu a 2027

Da aka tambaye shi ko zai iya sake rokon 'yan Najeriya su zabi APC a 2027, Keyamo ya ce nasarorin da jam'iyyar ta samu a zabukan baya-bayan nan sun tabbatar da karbuwarta.

Ya ce:

"Mun yi nasara a Ekiti. Mun ce mutane su kada kuri'a, suka kada, muka yi nasara. Haka ma a FCT suka kada kuri'a, muka yi nasara."

Lokacin da mai gabatar da shirin ya ambaci cewa Atiku Abubakar da Peter Obi za su kasance cikin 'yan takarar shugaban kasa a 2027, Keyamo ya ce hakan ba ya ba shi damuwa.

Ya ce:

"Tsakanina da kai, daga ina Peter Obi zai samo kuri'u? Ni ban ga hakan ba."

Ya kuma yi dariya lokacin da aka tambaye shi ko Atiku Abubakar zai iya zama barazana ga APC, inda ya ce:

Kara karanta wannan

APC ta fara zare ido ga wasu na kusa da Tinubu game da zaben 2027

"Wane Atiku? Barazana kuma?"
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a wajen taron APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Keyamo ya yi hasashen zaben 2027

A karshen hirar, Punch ta wallafa cewa Keyamo ya jaddada cewa yana da yakinin Tinubu zai sake lashe zabe.

Ya ce:

"Ina son in yi wata muhimmiyar magana. Ba don girman kai ko wuce gona da iri ba, amma saboda lissafin yawan masu kada kuri'a, zaben 2027 zai zama mai sauki.
"Ina maimaitawa, kada a cire maganata daga mahallinta, bisa lissafin yawan masu kada kuri'a, rantsarwa kawai muke jira."

A yanzu haka dai Bola Tinubu zai sake tsayawa takara karkashin jam'iyyar APC tare da mataimakinsa, Kashim Shettima.

APM ta soki Bola Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APM ta ce shugaba Bola Tinubu ya rasa goyon bayan 'yan Najeriya masu gaskiya saboda yadda gwamnatinsa ta gudanar da mulki.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa masu kira a sake zaben Tinubu a 2027 galibinsu 'yan siyasa ne da suka rasa amincewar jama'a kuma suna neman kariya daga zarge-zargen cin hanci da rashawa.

APM ta kuma yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu na daga cikin gwamnatocin da suka fi gazawa a tarihin Najeriya, saboda haka ba za ta samu sahihin goyon bayan jama'a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng