'Yan bindiga sun kallafa wa manoman jihar Katsina haraji
- Sakamakon yadda ta’addanci yake kara hauhawa a jihar Katsina, manoma da dama sun hakura da noma
- Hakan ya biyo bayan yadda ‘yan bindiga suka sanya musu haraji wanda suka wajabta wa manoman biya
- Gwamnatin jihar ta kiyasta gonaki 5,884 da masu noman su suka hakura saboda farmakin ‘yan bindiga
Katsina - Sakamakon hauhawar ta’addanci a fadin jihar Katsina, manoma da dama sun hakura da noma gonakin su sakamakon yadda ‘yan bindiga suka tilasta musu biyan harajin gonakin su.
Kamar yadda gwamnatin jihar Katsina ta kiyasta, gonaki 5,884 wadanda da ake noma wa aka dena saboda farmakin da ake kaiwa gonakin akai-akai.
Daga watan Janairu zuwa Yunin 2021 kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, an dakatar da noma hectare 23,333 na gonaki 2,924.
A karamar hukumar Danmusa a kauyen Gurzar-Kuka, Mara, Dunya da sauran kauyaku da ke kusa da dazuka suna fama da biyan haraji ga ‘yan bindiga idan za su yi anfani da gonakin su.
A wata tattaunawa da Daily Trust ta yi da dagacin Batsari, Alhaji Tukur Muazu, ya tabbatar da cewa shugabannin kauyaku 8 da ke Batsari sun tsere cikin birnin jihar Katsina don tsira daga ‘yan bindiga.
Kamar yadda ya ce:
“Babu mai zama a kauyen nan sai wanda ya biya ‘yan bindiga haraji ko kuma mai hada kai da su. Sun dakatar da manoma daga noma da kuma kiwon shanu. Dubbannin mutane sun gudu daga Batsari zuwa birane. Sai dai duk sun kama gidajen haya ne.
“Tunda muna da iyaka da jihar Zamfara, ‘yan bindiga da dama suna ta gudowa nan. Sun mamaye wuraren mu, ya ake so mu yi da wadanda suke tahowa daga Zamfara? Muna rokon gwamnati ta taimaka wurin yin abinda ya dace.”
Ya kara da bayyana cewa ya kwashe shekaru 3 ba tare da ya noma gonar sa ta hetare 2 ba saboda ‘yan ta’adda.
Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ‘yan kauyakun da ke karkashin karamar hukumar Batsari suke tilasta musu biyan haraji kafin siyan taki ko kuma yin aiki a gonakin su wadanda suka dade su na nomawa.
Akwai lokutan da sai manomi ya kammala noman sa, sai ‘yan bindiga su sako shanayen su don suyi huda a kan hatsin su wanda hakan ya ke janyo su lalata hatsin.
An rufe bankuna a jihar Ogun bayan 'yan fashi sun yi barazanar kai farmaki
A wani labari na daban, bankunan da ke Ijebu-Ode a jihar Ogun sun rufe sakamakon tsoron kada masu fashi da makamai su kai mu su farmaki.
Daily Trust ta ruwaito yadda masu shaguna suka rufe tun Litinin da safe bayan wasu wasiku da wasu da ake zargin ‘yan fashi suka tura wa wasun su.
Lamarin ya tsorata mazauna yankin yayin da abokan huldar bankunan suka shiga damuwa suka tsaya bakin bankunan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng