Ribadu: "Dabarar Gwamnati na Yaki da Ta'addanci Ya Fara Murkushe Yan Bindiga"
- Yayin da yan bindiga ke kai hare-haren kare dangi a wasu yankunan jihar Kaduna da wasu kauyuka a Najeriya, gwamnatin tarayya ta ce ta na kokari
- Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana irin nasoririn da gwamnatin Bola Tinubu ta samu wurin kare rayuka
- Ya buƙaci al'umma su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanan sirri domin suna da matukar muhimmanci wajen aikin kare rayukansu da dukiyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mallam Nuhu Ribadu, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), ya sake tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da kare rayukansu.
Ya ce ana kokari wajen murkushe ta'addanci ta hanyoyi da dama daga ciki har da ƙwace tare da lalata makaman da ake riƙe da su ba bisa ka'ida ba domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Ribadu ya bayyana haka ne yayin bikin lalata ƙananan makamai da makamai masu sauƙin ɗauka guda 2,819 da aka ƙwace.
Nuhu Ribadu ya halarci taron kona makamai
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa daga cikin makaman da aka kona akwai waɗanda aka daina amfani da su da kuma waɗanda suka lalace. An gudanar da bikin ne a Barikin Muhammadu Buhari Cantonment da ke Giri a Abuja.
Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin Ɗauka ta Ƙasa ce ta shirya wannan shiri, inda ta bayyana cewa adadin makaman da ta lalata tun bayan fara aikinta ya kai 19,000.
Ribadu, wanda Dr. Dennis Otuaro, shugaban Shirin Afuwa na Shugaban Ƙasa (PAP), ya wakilta, ya ce makaman da ake riƙe da su ba bisa ƙa'ida ba su ne ginshiƙin ayyukan 'yan ta'adda, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Ya ce:
"Kowane makamin da hukumomin tsaro suka ƙwato kuma suka lalata yana nufin an kawar da wata barazana har abada. Muna murƙushe barazana makami bayan makami."
Ribadu ya yi magana kan dabarun tsaro
Ribadu ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wata sabuwar dabarar tsaro da ta mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro, katse hanyoyin kuɗin masu laifi.

Source: Original
A cewarsa:
"Wannan tsari ya fara haifar da sakamako a sassan ƙasar nan, daga raunana ƙungiyoyin 'yan ta'adda zuwa ƙarfafa tsarin tsaron iyakokinmu, kuma ana ci gaba da inganta shi domin fuskantar sabbin barazana."
Ya ƙara da cewa lalata makaman da aka ƙwace na taimakawa ayyukan soji da sauran hukumomin tsaro ta hanyar rage yawan makaman da masu aikata laifuka za su iya amfani da su wajen tayar da tarzoma.
Asali: Legit.ng

