Tinubu Ya Fadi Abin da zai Yi wa 'Yan Najeriya idan Suna Biyan Haraji da Kyau

Tinubu Ya Fadi Abin da zai Yi wa 'Yan Najeriya idan Suna Biyan Haraji da Kyau

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a kara himma wajen biyan haraji, yana mai jaddada cewa dorewar samar da abubuwan more rayuwa ya dogaro da shi
  • Tinubu ya yi wannan kira ne a jiya yayin kaddamar da aikin titin da ya tashi daga mahadar Life Camp zuwa Ring Road III a yankin Dape na Babban Birnin Tarayya
  • Tinubu ya ce titin wani muhimmin aiki ne da aka yi domin inganta hanyoyin sufuri, rage cunkoson abubuwan hawa da kuma bude damammakin tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci mazauna da ‘yan kasuwa a babban birnin tarayya da su rika biyan haraji yadda ya kamata.

Ya yi magana yana mai cewa kudin shiga na gwamnati suna da muhimmanci wajen ci gaba da samar da abubuwan more rayuwa a babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe babban soja da wasu sojoji 7 a Kaduna

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da shugaba Bola Tinubu ke bayani a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa ya yi wannan kira ne a wajen kaddamar da titin Arterial Road N5 da ya hada mahadar Life Camp da Ring Road III a yankin Dape na Abuja.

Bayanin Bola Tinubu kan biyan haraji

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya wakilci shugaban kasar, inda ya ce wajibi ne ‘yan kasa su tallafa wa kokarin gwamnati ta hanyar biyan haraji.

“Ga mazauna da ‘yan kasuwa da ke cin moriyar wannan sauyi, ina kira gare ku da ku sauke nauyin da ya rataya a wuyanku. Ku biya harajinku.
“Ku biya kudin harajin filaye. Biyayyarku ce ke ba hukumar FCT damar gina karin hanyoyi irin wannan,”

In ji shi.

The Guardian ta rahoto Tinubu ya ce aikin titin ya nuna kudirin gwamnatinsa na kammala muhimman ayyuka maimakon barinsu.

Tinubu ya ce ya cika alkawari

A bayanin da ya yi, shugaban kasar ya tuna cewa ya yi alkawarin aikin yayin kaddamar da wani bangare na titin a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Shekaru 3 a kan mulki: An jero manyan ayyukan da Tinubu zai kaddamar a Abuja

“Na yi alkawarin ba zan bar wannan muhimmiyar hanya ba tare da an kammala ta ba.
“Saboda haka yau mun dawo. Mun dawo domin kammala aikin,”

In ji shugaban kasar.

Tinubu ya bayyana cewa an bayar da kwangilar aikin ne a watan Oktoban 2024 kuma an kammala shi cikin wa’adin da aka tsara, yana mai cewa hakan shaida ce ta sabuwar hanyar gudanar da ayyukan gwamnati.

Sabon titin da aka yi a Abuja
Titin da shugaba Bola Tinubu ya kaddamar a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Amfanin titin da Tinubu ya yi

Tinubu ya kara da cewa sabon titin zai saukaka zirga-zirga tsakanin Dape, Karmo, Gwarinpa, Kado, Mbora da Idu, tare da samar da damammakin tattalin arziki ta hanyar saukaka isa masana’antu da kasuwanni.

“Baya ga haka, wannan hanya ta bude wata damar isa yankin masana’antu na Idu kai tsaye. Wannan zai rage kudin sufuri ga ‘yan kasuwa,”

In ji shi.

Tinubu ya gargadi 'yan ta'adda

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na kara kaimi wajen yaki da rashin tsaro

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya jinjina wa Tinubu, ya ce 'yan Arewa za su saka masa da kuri'u a 2027

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ne ya isar da sakon Tinubu yayin taron addu’ar Kirista da aka gudanar a bikin ranar dimokuradiyya.

A wata sanarwa da Sanata Akume ya ftar, Tinubu ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta taba mika wuya ga 'yan ta’adda da ‘yan bindiga ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng