Ginin Tituna
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da s rika biyan haraji da kyau domin samun damar ayyukan cigaba mai dorewa. Ya fadi haka ne a birnin Abuja.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai fara kaddamar da manyan ayyukan more rayuwa a Abuja daga ranar Talata.
Ministan Ayyuka a Najeriya, David Umahi, ya bai wa masu kwangilar gyaran hanyar Abuja zuwa Lokoja wa'adin sa'o'i 72 su koma aiki ko su fuskanci EFCC.
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da aikin sake gina babbar hanyar Gombe zuwa Biu da Maiduguri, bayan shekaru masu yawa na alkawura da kwangilolin da ba su kammala ba.
A labarin nan, za a ji cewa David Umahi, Wanda shi ne ministan ayyuka a Najeriya ya bayyana yadda Bola Tinubu ya yi rabon aikin tituna tsakanin Arewa da Kudu.
A labarin nan za a ji cewa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da nasarorin da gwamnatinsa a samu a cikin shekaru uku na mulkin kasar nan.
FRSC ta shawarci matafiya su sauya hanyar da suke bi daga Abuja zuwa Kaduna yayin da aka samu cunkoso a tsakanin Nasarawa da Azaga, daga Katari zuwa Jere.
Gwamna Dikko Radda ya ƙaddamar da titin Ingawa–Dutsi–Shargalle mai tsawon 39km a Katsina domin bunƙasa kasuwanci da sauƙaƙa zirga-zirga a yankin.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta damƙa kwangilar gyara tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin Can ga kamfanin aminin sa, Gilbert Chagoury, a kan dala biliyan 1.
Ginin Tituna
Samu kari