NSIPA: Matar da Tinubu Ya Kora Ta Rubuta Masa Wasiƙa bayan Wahalar da Ta Sha
- Tsohuwar shugabar NSIPA, Halima Shehu, ta rubuta wasika ta musamman ga Shugaban kasa, Bola Tinubu
- Halima ta roki Tinubu da ya umarci EFCC ta fitar da rahoton binciken zarge-zargen da aka yi mata domin wanke sunanta
- Ta ce ta gano almundahanar kuɗi da matsalolin gudanarwa a NSIPA, sannan ta kai ƙorafi ga ICPC kafin dakatar da ita daga mukaminta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohuwar shugabar Hukumar Kula da Shirye-shiryen Zuba Jarin Jama'a ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu, ta roƙi Shugaba Bola Tinubu.
Halima ya bukaci Tinubu da ya umarci Hukumar EFCC ta fitar da rahoton binciken da ta gudanar kan zarge-zargen da aka yi mata.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta aika wa shugaban ƙasa wacce jaridar TheCable ta samu.
NSIPA: Musabbabin dakatar da Halima Shehu
An dakatar da Halima daga mukaminta a watan Janairun 2024 bayan zargin karkatar da kuɗaɗe da rashin bin ƙa'idojin gudanarwa a NSIPA.
Daga baya EFCC ta gayyace ta domin yi mata tambayoyi, amma har yanzu ba a fitar da sakamakon binciken ba.
Halima ta yi karin haske kan zarge-zarge
Halima ta ce fitar da rahoton EFCC zai wanke sunanta tare da tabbatar da cewa ba ta aikata abin da ake zarginta da shi ba.
Ta bayyana cewa ta yi ƙasa da watanni huɗu tana jagorantar NSIPA kafin dakatar da ita, tana mai cewa zarge-zargen almundahanar kuɗi da aka yi mata ƙarya ne da suka jawo mata da iyalanta matsanancin raɗaɗin zuciya da lalacewar suna.
Halima ta ce tun kafin dakatar da ita ta gano manyan matsalolin kuɗi da raunanan hanyoyin sa ido a hukumar.
Saboda haka, ta kai rahoton zargin ga ICPC tare da gabatar da hujjoji a ranar 22 ga Disamba, 2023.
Ta ƙara da cewa kwanaki kusan 10 bayan kai rahoton, aka dakatar da ita daga aiki ba tare da an ba ta amsa daga hukumomin yaƙi da cin hanci ba.
Haka kuma, ta yi zargin cewa an cire kusan Naira biliyan 14 daga asusun hukumar ba tare da saninta ba, cewar Daily Post.

Source: Facebook
Halima Shehu ya wanke kanta daga zargi
A cewarta, an saka wasu mutane a matsayin masu sa hannu a asusun Remita na NSIPA da ke Babban Bankin Najeriya (CBN) ba tare da izninta ba, lamarin da ya sa aka gudanar da wasu mu'amaloli ba tare da amincewarta ba.
Halima ta ce EFCC ba ta ƙwato ko kwabo daga wajenta ba, tana mai cewa ta rubuta wasiƙu da dama ga EFCC da gwamnatin tarayya tana neman a kammala binciken tare da wallafa rahotonsa domin gaskiya ta fito fili, ta kuma ce hakan zai dawo mata da mutunci tare da ƙarfafa mata masu sha'awar shugabanci.
NSIPA ta yi tone-tone kan tsohuwar minista
A baya, an ji cewa hukumar jin dadin al'umma ta kasa (NSIPA) ta yi watsi da badakalar kudi da aka yi wa ministar jin kai, Betta Edu.
Shugaban sashin sadarwa na NSIPA, Jamaludeen Kabir, ya nesanta hukumar daga zargin da ke alakanta Edu da badakalar NSIPA.
Kabir ya kara da cewa ministar ba ta da hannu a duk wani hada-hadar kudi ko yanke hukunci a hukumar NSIPA.
Asali: Legit.ng


