Gwamna Bala Ya Kayyade Sadakin Zawarawa zuwa N1,500 a Bauchi? Gaskiya Ta Fito
- Gwamnatin Bauchi ta musanta rahoton da ke cewa Gwamna Bala Mohammed ya amince da sadakin N1,500 ga matan da aka saki
- Kwamishina Muhammad Binni ya ce bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙarya ce da aka ƙirƙira domin yaudarar jama'a
- Gwamnati jihar ta bukaci jama'a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su domin kare zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Bauchi – Gwamnatin jihar Bauchi ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa Gwamna Bala Mohammed ya amince da sanya sadakin N1,500 ga matan da aka saki.
Kwamishinan Harkokin Addini da Wayar da Kan Al'umma, Muhammad Binni, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi ranar Lahadi, inda ya ce rahoton ƙarya ne kuma an ƙirƙire shi ne domin yaudarar jama'a.
Bidiyon da ke yawo ba shi da tushe
Binni ya ce bidiyon da ke yawo a Facebook da TikTok ya kuma yi ikirarin cewa Sarkin Zar (Gum Zar) ya umarci al'umma su bi wannan manufar da ake zargin gwamnati ta fito da ita, in ji rahoton Punch.
Sai dai ya bayyana zargin a matsayin ƙarya tsagwaronta, mara tushe kuma ƙagagge.
Ya ce:
"Gwamnatin jihar Bauchi ba ta taɓa fitar da wata doka ko tsari da ya shafi sadakin matan da aka saki ko mata marasa aure ba. Bayanin da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙarya ce da aka ƙirƙira domin yaudarar jama'a."
An bukaci jama'a su guji yaɗa jita-jita
Kwamishinan ya roƙi mazauna jihar da su yi watsi da bidiyon tare da kauce wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da ingancinsu ba, yana mai cewa hakan na iya haddasa ruɗani da tayar da hankalin jama'a.
Ya kuma jaddada cewa tun bayan hawansa mulki, Gwamna Bala Mohammed yana mutunta addini, al'adu da kuma dabi'un al'ummar Bauchi, kuma gwamnati ba za ta taɓa aiwatar da manufofin da suka saɓa wa waɗannan ƙimomi ba.
Gargadi ga masu amfani da soshiyal midiya
Muhammad Binni ya buƙaci jama'a su rika tantance sahihancin duk wani bayani kafin su wallafa ko su tura shi ga wasu.
A cewarsa, yaɗa ƙarya na iya kawo cikas ga zaman lafiya, haɗin kan al'umma da kuma mutuncin jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa wani mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Boroh James Hussaini ne ya yi iƙirarin cewa za a sanya sadakin N3,000 ga budurwar da ta taɓa haihuwa ba tare da aure ba, sannan ya ce za a aurar da mata marasa aure da suka daɗe ba tare da haihuwa ba ga direbobi ba tare da an biya sadaki ba, zargin da gwamnatin Bauchi ta ce ba shi da gaskiya.
Asali: Legit.ng

