Bayan Shafe Watanni Ana Kai Ruwa Rana, Iran da Amurka Sun Kawo Karshen Hare Hare

Bayan Shafe Watanni Ana Kai Ruwa Rana, Iran da Amurka Sun Kawo Karshen Hare Hare

  • DrKasar Iran da Amurka sun dakatar da hare-haren juna na kwanaki biyu, yayin da gwamnatin Donald Trump ta ba da damar tattaunawa
  • Iran ta ce ta dakatar da ramuwar gayya kan kawayen Amurka, yayin da jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da shirin ci gaba da tattaunawa
  • Duk da dakatar da hare-haren, Benjamin Netanyahu ya bukaci Trump ya tabbatar da kawo karshen shirin nukiliyar Iran, ta hanyar yarjejeniya ko matakin soja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka sun dakatar da hare-haren juna a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin 2026.

Hakan ya ba da damar zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Fasha da masana'antar mai damar samun sauki bayan kwanaki na musayar hare-hare.

Iran da Amurka sun tsagaita wuta
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

An dakatar da hare-hare tsakanin Amurka, Iran

Iran ta sanar da cewa ta dakatar da hare-haren ramuwar gayya kan kawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya, cewar BBC News.

Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Mike Waltz, ya ce Shugaba Donald Trump yana ba tattaunawa damar ci gaba.

Kafin ranar Juma'a, sojojin Amurka sun kai hare-hare kan Iran na dare goma sha uku a jere.

Mai magana da yawun rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya ce Amurka ta dakatar da hare-haren nata, saboda haka Iran ma ta dakatar da matakan ramuwar gayya.

Rikicin da ya shafi mashigar ruwa na Hormuz ya dagula kokarin sasanci tsakanin Tehran da Washington.

Rahotannin kafafen yada labaran Iran da ba a tabbatar da su ba sun ce wani jirgin dakon mai ya lalace sakamakon wani bam da aka dasa a cikin teku.

Sai dai wasu rahotannin Amurka sun ce hakan na iya kasancewa saboda karancin makaman kariya.

Mike Waltz ya musanta wannan zargi, yana mai cewa sojojin Amurka na da dukkan kayan aikin da suke bukata domin ci gaba da gudanar da duk wani mataki idan ya zama dole.

Netanyahu zai je Amurka
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Netanyahu zai gana da Trump

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gana da Trump a Fadar White House da ke kasar Amurka a ranar Talata, ana sa ran zai bukaci shugaban Amurka ya ci gaba da daukar tsauraran matakai kan Iran.

Netanyahu ya ce zai goyi bayan duk wani yunkurin Trump na kawo karshen shirin nukiliyar Iran, cewar Punch.

Rahoton New York Times ya ce an dakatar da shirin kara zafafa hare-haren saboda raguwar wasu makaman kariya, yayin da Trump ke fuskantar matsin lamba daga rikicin.

Trump ya ce har yanzu ana tattaunawa da Iran kuma yana ganin bangaren Tehran na kara nuna muhimmancin cimma matsaya ta diflomasiyya.

Yayin da rikicin ke ci gaba da shiga wata na biyar, mazauna Tehran sun koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum duk da tsananin zafi da cunkoson ababen hawa.

A wani bangare kuma, 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran sun ce sun harbo jirgin yaki marar matuki na Saudiyya, bayan sun kai hari kan cibiyoyin man Aramco.

Amurka za ta janye tallafi ga Najeriya

Mun ba ku labarin cewa Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da duk tallafin Amurka ga ƴan Najeriya da kasar baki daya.

Masana sun gargadi cewa idan kudirin ya zama doka, shirye-shiryen HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, rigakafi da lafiyar mata da yara za su shiga hadari.

Sun bukaci gwamnatin Najeriya ta inganta tsaro, karfafa dangantaka da Amurka, tare da samar da hanyoyin cikin gida domin daukar nauyin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com