Juyin Mulki: DSS Ta Kai Wanda ake Zargi da Zuga Sojoji gaban Kotu

Juyin Mulki: DSS Ta Kai Wanda ake Zargi da Zuga Sojoji gaban Kotu

  • Hukumar DSS ta gurfanar da wani mutum a kotun tarayya bisa zargin kira da a hambarar da gwamnatin Shugaba Tinubu ta hanyar juyin mulki
  • Ana zargin Paul Jibrin Oweleke ya yi amfani da kafarsa ta sada zumunta mai suna wajen wallafa saƙonnin da suka tunzura jama'a da sojoji
  • Kotu ta fara zama a kan wannan zargin, yayin da ake ci gaba da duba yunkurin tunzura jami'an tsaro su yi wa gwamnatin da aka zaba bore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas – Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wani mutum mai suna Paul Jibrin Oweleke a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

An gurfanar da mutumin ne bisa zargin amfani da kafafen sada zumunta wajen kira da a yi juyin mulki domin kawar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, daga mulki.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

DSS ta fara shari'a da wanda ke neman sojoji su hambarar da gwamnatin Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, alamar hukumar SSS Hoto: Bayo Onanuga/DSS Unofficial
Source: Twitter

A rahoton jaridar Punch, an gurfanar da Oweleke a ranar Litinin 8 ga watan Yuni, 2026 a gaban Mai Shari'a Akintoye Aluko kan tuhume-tuhume guda biyu.

DSS ta kai Oweleke kotu

A ruwayar Thisday, an kai Paul Jibrin Oweleke bisa zargin aikata laifuffukan yanar gizo da kuma aika saƙonnin da ake zargin za su iya haddasa rikici da tayar da tarzoma a cikin al'umma.

Lauyan DSS, Michael Bajela, ya shaida wa kotu cewa hukumar ta shigar da tuhume-tuhume biyu a kan wanda ake zargin, tare da neman a karanta masa laifuffukan domin ya amsa.

A cewar DSS, wanda ake zargin ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta mai suna “Oweleke TV” wajen wallafa saƙonni da shirye-shiryen watsa labarai da ke kira ga sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu .

Ya ba su shawarwarin cewa ya kama su yi kwaikwayon abubuwan da suka faru a ƙasar Burkina Faso a nan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun baza koma bayan an kama ɗan sandan ƙasar waje da bindiga a Katsina

Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Oweleke ya musanta duka zarge-zargen da ake masa na cewa yana tunzura jama'a domin a yi juyin mulki.

Zargin da DSS ke yi wa Oweleke

DSS ta kuma yi zargin cewa wanda ake ƙarar ya aika wasu saƙonni da suka ƙunshi barazana, cin zarafi ko tsoratarwa ga Shugaba Tinubu.

Hukumar ta ce laifuffukan da ake zargin ya aikata sun saɓa da tanade-tanaden dokar hana cin zarafi ta yanar gizo ta shekarar 2015 da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2024.

DSS ta ce Owelele zai iya tayar da tarzoma da sakonninsa
Wasu daga cikin jami'an hukumar DSS a bakin aiki Hoto: DSS Unofficial
Source: Twitter

Bayan Oweleke ya musanta zarge-zargen, Bajela ya roƙi kotu ta sanya ranar fara shari'a tare da umartar a tsare shi a gidan gyaran hali har sai an kammala shari'ar.

Sai dai lauyan wanda ake ƙara ya sanar da kotu cewa ya riga ya shigar da takardar neman beli ga wanda yake karewa, kuma an bai wa masu gabatar da ƙara kwafin buƙatar.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari'a Aluko ya ɗage shari'ar zuwa ranar 16 ga Yuni, 2026 domin sauraron buƙatar beli, tare da umartar a ci gaba da tsare Oweleke har zuwa lokacin.

Kara karanta wannan

Auren gata: Abin da Hisbah za ta yi wa maza da mata 3,000 a Kano kafin a biya sadaki

Yadda aka shirya juyin mulki

A wani labarin, mun wallafa cewa rundunar sojin Najeriya ta yi bayanin yadda aka gano shirin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayin gabatar da shaida a kotu.

Wani soja daga rundunar ‘yan sandan sojoji (NACMP), wanda kotu ta boye sunansa, ya bayar da shaida a shari'ar mutane shida da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin tarayyar Najeriya.

Binciken ya kuma gano wani kamfani mai suna Purple Wave wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen daukar nauyin shirin juyin mulkin da jami'an tsaro suka yi gaggawar dakile wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng