Shugaba a Majalisa Ya Faɗi Lokacin da za a Amince da Dokar Ƴan Sandan Jihohi

Shugaba a Majalisa Ya Faɗi Lokacin da za a Amince da Dokar Ƴan Sandan Jihohi

  • Majalisar Tarayya na shirin amincewa da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi bayan an kara wa kudurin sauri biyo bayan karuwar rashin tsaro
  • Shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Opeyemi Bamidele ya ce an kammala tattaunawa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki
  • Bayan amincewar Majalisa, ana bukatar akalla kashi biyu bisa uku na majalisun jihohi su tabbatar da kudirin da zai ba gwamnoni damar tafi da yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa Majalisar Tarayya za ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi a makon nan.

Sanata Bamidele ya bayyana cewa ana shirin amincewa da dokar, wacce idan ta tabbata, za ta mika ragamar kula da harkokin yan sanda ga gwamnoni.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi murna da ceto mutane 360, ya ce sojoji za su iya murkushe ta'addanci a Najeriya

Majalisar Dattawa ta yi magana a kan dokar yan sandan jihohi
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele a taron masu ruwa da tsakin APC Hoto: @senate_leader
Source: Twitter

Premium Times ta ruwaito cewa Bamidele, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki na Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 9 ga watan Yuni, 2026.

Bamidele: Majalisa ta damu da rashin tsaro

A ruwayar jaridar The Cable, Opeyemi Bamidele, Ya ce matakin na daga cikin kokarin da Majalisar Tarayya ke yi domin samar da mafita ga matsalolin tsaro da suka addabi sassan kasar nan.

A cewarsa, da zarar Majalisar Tarayya ta amince da kudirin, za a mika shi ga majalisun dokokin jihohi 36 domin tantancewa da tabbatarwa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Sanata Bamidele ya ce:

“Mun cimma matsaya cewa za mu amince da gyaran kundin tsarin mulki domin samar da tanadin kafa ‘yan sandan jihohi, kuma zan iya tabbatar muku cewa hakan zai kasance a wannan makon saboda babu dalilin ci gaba da jinkirta lamarin.”

Kara karanta wannan

Amurka ta gamu da matsala, jirgin yakinta ya rikito a kusa da mashigar Hormuz

Ana shiri kan dokar yan sandan jihohi

Opeyemi Bamidele ya kara da cewa a cikin makonnin baya-bayan nan, shugabannin Majalisar Tarayya sun gudanar da taruka da dama tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sauran wadanda aka zauna da su a taron sun hada da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban masu rinjayen ya bayyana cewa batun kafa ‘yan sandan jihohi ne zai mamaye muhawarar Majalisar Tarayya a wannan makon saboda muhimmancinsa ga tsaron kasa.

Majalisar dattawa za ta aika dokar kafa yan sandan jihohi ga majalisun jihohi
Sanataci yayin da aka tashi a zauren majalisar dattawa da ke Abuja Hoto: Nigerian Senate
Source: Twitter

Ya ce an ware kudirin daga sauran gyare-gyaren kundin tsarin mulki domin a gaggauta kada kuri’a a kansa tare da tura shi zuwa majalisun jihohi.

A cewarsa, ana bukatar akalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi su amince da kudirin kafin a aika wa Shugaba Tinubu domin sanya hannu.

Gwamna ya goyi bayan batun yan sandan jihohi

A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana matsayarsa kan batun kafa 'yan sandan jihohi da ake ta muhawara a kai domin kawo karshen matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya

Dikko Umaru Radda PhD ya goyi bayan kafa 'yan sandan jihohi domin yaki da matsalar rashin tsaron da ake ta fama da ita a sassan Najeriya, musamman jihohin da ke Arewacin kasar nan.

Gwamnan ya kuma yi watsi da fargabar cewa kafa 'yan sandan jihohin zai ba gwamnoni damar muzgunawa abokan hamayya, inda ya ce tsarin zai taimaka matuka wajen magance batun tsaron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng