Babbar Magana: NLC Ta Haifar da Matsala, Ta Hana Jirgin Sama Tashi a Najeriya
- Zanga-zangar kungiyar kwadago ta NLC ta kawo cikas ga zirga-zirgar jirage a filin jirgin sama na jihar Legas
- Rahotanni sun nuna cewa kungiyar NLC ta haifar da tangarda, wanda ya hana jirgin sama na kamfanin Air Peace tashi kamar yadda aka tsara
- Wata majiya ta ce zanga-zangar na da alaka da bukatar ma’aikatan Air Peace su shiga kungiyar kwadago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legas, Nigeria - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta kawo cikas ga zirga-zirgar jirage a Legas a yau Talata, lamarin da ya sa fasinjojin wani jirgin Air Peace suka makale a filin jirgin saman.
An ce zanga-zangar ta fara ne da misalin karfe 5:00 na asuba, inda aka kulle kofar tashar Zulu, lamarin da ya hana fasinjoji shiga domin ci gaba da shirye-shiryen tafiyarsu.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Source: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta rahoto ceewa jirgin Air Peace da abin ya shafa an tsara zai tashi daga Legas da misalin karfe 6:30 na safe, amma bai samu damar tashi ba sakamakon katsewar ayyukan filin jirgin.
Fasinjoji sun makale a Legs
Matakin kungiyar NLC ya haifar da takaici da rashin tabbas tsakanin fasinjojin da suka isa filin jirgin da wuri domin tafiya.
Daya daga cikin fasinjojin da ya yi magana ya ce jinkirin ya dagula masa shirye-shiryen tafiya, yana mai cewa bai san lokacin da jirgin zai samu damar tashi ba.
Wata fasinja kuma ta ce ta isa filin jirgin da wuri domin jirgin da aka tsara zai tashi da karfe 6:30 na safe, amma ta samu kanta cikin yanayin rashin tabbas ba tare da cikakken bayani kan lokacin da ayyukan jirage za su dawo ba.
Kamfanin Air Peace ya tabbatar da lamarin

Kara karanta wannan
Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Da aka tuntubi wani ma’aikacin kamfanin sufuri na Air Peace domin jin halin da ake ciki, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Eh, gaskiya ne,” amma ya ki bayyana dalilin zanga-zangar.
Sai dai wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana cewa zanga-zangar na da alaka da batun kungiyar kwadago, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
A cewar majiyar, manufar zanga-zangar ita ce tilasta wa Air Peace mutunta hakkin ma’aikatanta na shiga kungiyar kwadago.
NLC ta hanyar zanga-zangar ta kawo tsaiko ga harkokin sufuri a filin jirgin saman, yayin da fasinjojin da abin ya shafa ke ci gaba da jiran karin bayani kan lokacin da jirage za su tashi.
Jirgin Enugu Air ya yi saukar gaggawa
A wani rahoton, kun ji cewa fasinjoji 68 sun shiga firgici bayan jirgin Enugu Air ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Benin a jihar Edo.
Wata majiya a filin jirgin saman Benin ta shaida cewa jirgin ya wuce karshen titin saukar jirgi bayan sauka, sannan ya shiga wani daji da ke kusa.
Majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce jami’an Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) sun yi hanzarin kwashe dukkan fasinjojin daga jirgin cikin aminci.
Asali: Legit.ng