Saura Ƙiris: Fadar Shugaban Kasa Ta Kwantar da Hankula kan Ƴan Sandan Jihohi

Saura Ƙiris: Fadar Shugaban Kasa Ta Kwantar da Hankula kan Ƴan Sandan Jihohi

  • Fadar Shugaban Kasa a Najeriya ta yi karin haske game da shirin kafa ƴan sanda a fadin jihohin kasar
  • Gwamnatin ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kafa ‘yan sandan domin inganta tsaro a kasar
  • An ce tattaunawar kafa ‘yan sandan ta fara watanni da suka gabata bisa umarnin Bola Tinubu, yanzu ya kai matakin gyaran doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tsarin ‘yan sandan jihohi zai inganta tsaro da tattara bayanan sirri.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen shirin kafa ‘yan sandan jihohi.

Shirin kafa yan sandan jihohi ya kankama a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Sufeta-janar na ƴan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a X.

Matakin da ake kan kafa yan sandan jihohi

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wani taron tattaunawa kan batun ‘yan sandan jihohi da Fadar Shugaban Kasa ta shirya a Abuja.

A cewarsa, tattaunawar samar da tsarin ‘yan sandan jihohi ta fara watanni uku zuwa hudu da suka gabata bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, kuma yanzu an kai matakin duba gyaran kundin tsarin mulki.

Sanarwar ta ruwaito Gbajabiamila yana cewa batun kafa ‘yan sandan jihohi na bukatar zurfin nazari kan kundin tsarin mulki da dokoki.

Ya ce:

"Mun fara tattaunawa watanni uku ko hudu da suka gabata kan yadda za a kafa ‘yan sandan jihohi kamar yadda shugaban kasa ya umarta.
“Kafa ‘yan sandan jihohi ba abu ne da za a yi cikin gaggawa ba. Akwai abubuwa masu yawa da suka shafi kundin tsarin mulki da dokoki, kuma mun samu ci gaba sosai yanzu.”
Ana shirin kafa yan sandan jihohi saboda inganta tsaro
Babban sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Shirin da ake yi kan yan sandan jihohi

Gbajabiamila ya bayyana cewa a halin yanzu hankalinsu yana kan gyaran kundin tsarin mulki, sannan daga baya za a samar da dokokin da za su ba tsarin damar aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Bai da maraba da Buhari': An caccaki tsarin siyasar Peter Obi a Najeriya

Ya ce bayan doguwar tattaunawar da aka yi ta mayar da hankali ne kan yadda za a tsara gyaran kundin tsarin mulkin da kuma dokokin da za su biyo baya.

Rahoton ya nuna cewa batun kafa ‘yan sandan jihohi ya sake samun karbuwa sakamakon matsalolin tsaro da suka hada da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ‘yan bindiga da ake fama da su a sassan kasar.

Masu sukar tsarin ‘yan sanda na kasa sun dade suna cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi wa kanta nauyi sosai, tana fama da karancin kayan aiki kuma ta yi nesa wasu yankuma masu matsaloli.

Gbajabiamila ya ce yanzu an samu fahimtar juna a fadin kasa kan bukatar kafa ‘yan sandan jihohi, inda tattaunawa ta wuce matakin ko za a yi tsarin zuwa yadda za a aiwatar da shi.

Gwamnatin tarayya ta nemo hanyar dakile matsalar tsaro

Mun ba ku labarin cewa ministan yaɗa labarai a Najeriya, Mohammed Idris, ya ba yan Najeriya shawara game da karuwar hare-hare a kasar.

Mohammed Idris ya buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in tashin hankali a kasar.

Ministan ya ce cin nasarar yaƙi da ta’addanci na buƙatar haɗin kan ƙasa baki ɗaya ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini, ƙabila ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.