Abin Mamaki: Gwamna Ya Fadi Yadda Yake Hada Tika Rawa da Aikin Ofis
- Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ce sha'awar rawa da yake da ita ba ta hana shi sauke nauyin da ke kansa a matsayin gwamna ba
- Adeleke ya ce rawa wani bangare ne na halayensa da kuma abin sha'awa, yana mai cewa ya gudanar da ayyukan raya jihar a fannoni daban-daban
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu neman takarar gwamnan Osun da aka shirya gabanin zaɓen ranar 15 ga Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Osogbo – Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya kare rawan da ya ke yi, yana mai cewa hakan ba ya hana shi sauke nauyin da ke kansa a matsayin gwamnan jihar.
Adeleke ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani taron ‘yan takarar gwamnan Osun da Arise TV ta shirya gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.

Kara karanta wannan
Hadimin Buhari zai bude babin 2023 ya tona abin da ya faru lokacin neman takarar APC

Source: Instagram
Adeleke zai rika tika rawa
Punch ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana kansa a matsayin mutum mai aiki da hankali, yana mai cewa rawa wani bangare ne na halayensa da kuma abin da yake jin daɗin yi.
Ya ce yana rawa saboda irin yanayin iyalinsa, amma hakan ba ya hana shi gudanar da ayyukan gwamnati.
"Ina rawa ne saboda a cikin iyalina, mu mutane ne masu farin ciki. Yayin da nake rawa, ina aiki. Akwai lokacin komai, akwai lokacin rawa kuma akwai lokacin aiki."
Ya ƙara da cewa rawa ba ya hana shi yin ayyukan da aka zaɓe shi domin yi, yana mai cewa ya gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban na jihar.
Adeleke ya kare gwamnatinsa
Gwamna Adeleke ya ce gwamnatinsa ta gina tare da gyara hanyoyi a sassa daban-daban na jihar Osun.
Ya ce an kuma sanya fitilun tituna masu amfani da hasken rana a wasu daga cikin hanyoyin domin ƙara tsaro da bunkasa harkokin tattalin arziƙi.
Leadership ta wallafa cewa ya ce:
"Ina magana da ku yanzu, ba wai na gina hanyoyi a faɗin Osun kaɗai ba, na kuma sanya musu fitilun kan hanya masu amfani da hasken rana."
An gyara cibiyoyin lafiya
Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta gyara tare da inganta cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko sama da 200.
Ya ce an samar wa cibiyoyin wutar lantarki da tsaftataccen ruwan sha domin inganta ayyukan kiwon lafiya ga al'umma.
Adeleke ya ce:
"Ya zuwa yau, mun inganta tare da gyara cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko sama da 200 zuwa matakin da ya dace da ƙa'idojin duniya."

Source: Twitter
Atiku ya dura jihar Osun
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya ce jam'iyyar ta zama mafi dacewa a Najeriya.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Osogbo yayin babban taron yaƙin neman zaɓen ADC, inda ya nemi magoya bayan jam'iyyar su zaɓi ɗan takararta na gwamna, Najeem Salaam.
Ya ce ADC ta bambanta da APC, Accord da sauran jam'iyyun siyasa, yana mai kira ga al'ummar Osun da su zaɓi jam'iyyar a zaɓen ranar Asabar.
Asali: Legit.ng
