Gwamna Radda Ya Goyi Bayan Kafa 'Yan Sandan Jihohi, Ya Kawo Dalilai
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana matsayarsa kan batun kafa 'yan sandan jihohi da ake ta mahawara a kai
- Dikko Umaru Radda ya goyi bayan kafa 'yan sandan jihohi domin yaki da matsalar rashin tsaron da ake ta fama da ita
- Gwamnan ya kuma yi watsi da fargabar cewa kafa 'yan sandan jihohin zai ba gwamnoni damar muzgunawa abokan hamayya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce yana goyon bayan kafa rundunar ’yan sandan jihohi.
Gwamna Radda ya ce yana goyon bayan hakan ne saboda ingantaccen aikin ɗan sanda yana buƙatar haɗin gwiwa da al'ummomi.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da wasu manyan jami’an kafafen yaɗa labarai lokacin gudanar da ziyarar gani da ido na ayyukan da gwamnatinsa ta yi tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023.
Radda na son a kare rayuka da dukiyoyi
Gwamna Radda ya jaddada cewa yana da kyau a dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sakamakon amincewa da irin rawar da ingantaccen aikin ɗan sanda ke takawa wajen kare rayukan ’yan ƙasa, Radda ya bayyana cewa tsaro ya kasance babban nauyi na gwamnati, jaridar The Guardian ta kawo rahoton.
"Tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne jigon gwamnati. Idan ya dace, kada a yi kasa a gwiwa wajen kashe kowane irin kuɗi domin ceto rayukan ’yan ƙasa. Ba za ka iya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ba tare da sako ’yan ƙasa a ciki ba."
“Mun ’yantar da ƙananan hukumomi da dama waɗanda a da suke ƙarƙashin ikon ’yan bindiga. Ƙila ba mu samu nasara 100% ba a yaƙin da muke yi da ta’addanci, amma mun sake ƙwato ikon ƙananan hukumomin da a da can suke ƙarƙashin firgici na waɗannan gungun masu laifi."
- Gwamna Dikko Radda
Me Radda ya ce kan 'yan sandan jihohi?
Ya jaddada bukatar kafa ’yan sandan jihohi domin bai wa jihohi damar tunkarar ƙalubalen da rashin tsaro ke haifarwa, sannan ya yi watsi da fargabar cewa gwamnoni za su karkatar da amfanin ’yan sandan jihohin inda ya bayyana hakan a matsayin mara tushe.
“Na san wasu mutane sun yi watsi da kiraye-kirayen kafa ’yan sandan jihohi saboda sun yi amanna cewa hakan zai bai wa gwamnoni damar amfani da su wajen yaƙar abokan hamayya na siyasa."
"Kamata ya yi ku tuna cewa mafi yawancin lokacin da gwamnoni za su iya yi a kan mulki shekaru takwas ne. Da zaran wa’adin mulki biyu ya ƙare, har yanzu ana iya gurfanar da gwamnonin domin su fuskanci fushin doka akan kowane irin keta doka ko zarge-zarge.”
- Gwamna Dikko Radda

Source: Facebook
Gwamna Radda ya samu tikitin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya samu tikitin APC domin yin takara a karo na biyu a 2027.
Gwamna Dikko Ummaru Radda ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Katsina domin neman tazarce a zaɓen 2027.
Wakilan jam’iyyar APC ne suka tabbatar da Gwamna Dikko Radda a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2027 ta hanyar maslaha.
Asali: Legit.ng


