Magana Ta Girma: Gwamnatin Tinubu Za Ta Kwaso ’Yan Najeriya a Afirka Ta Kudu

Magana Ta Girma: Gwamnatin Tinubu Za Ta Kwaso ’Yan Najeriya a Afirka Ta Kudu

  • Gwamnatin tarayya ta nunu damuwa game da rikicin da ke faruwa a Afirka ta Kudu wanda ya jawo asarar rayukan yan Najeriya
  • Kasar ta fara shirye-shiryen kwaso ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu bayan zanga-zangar kyamar baki da hare-haren da suka kara tsananta
  • Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce gwamnati ba za ta zura ido tana kallon cin zarafi da kashe ‘yan Najeriya ba tare da daukar mataki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen kwaso ‘yan Najeriya da suke son dawowa gida daga Afirka ta Kudu bayan sababbin hare-hare.

Matakin ya biyo bayan hare-haren kyamar baki da suka barke a wasu yankunan kasar musamman kan 'yan Najeriya.

Gwamnatin Tinubu za ta kwaso yan Najeriya a Afirka ta Kudu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta bayyana hakan bayan tattaunawar waya da ministan hulda da kasashen duniya na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola wanda ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Iran ta lalata jiragen Amurka bayan kasar ta kai mata hari a mashigar Hormuz

Najeriya ta fusata kan rikici a Afirka ta Kudu

Ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba za ta iya ci gaba da kallon yadda ake cin zarafin ‘yan kasarta da kuma kashe wasu ba bisa ka’ida ba.

Bianca ta ce duk da cewa ministan Afirka ta Kudu ya nuna damuwa kan batun kwaso ‘yan Najeriya, gwamnatin Najeriya ta fifita kare rayukan ‘yan kasarta.

Ta kuma bukaci hukumomin Afirka ta Kudu su dauki matakin gaggawa kan rahotannin kashe ‘yan Najeriya tare da hukunta masu hannu a ciki.

A cewarta, zanga-zangar da aka gudanar a Durban ba ta rikide zuwa tashin hankali ba saboda yadda jami’an tsaro suka bazama a yankin.

Sai dai ta ce ofishin jakadancin Najeriya ya shawarci ‘yan Najeriya da su rufe kasuwancinsu tare da zama a gida domin kare lafiyarsu.

An shirya daukar mataki bayan kisan yan Najeriya a Afirka ta Kudu
Shugaba Bola Tinubu da ministar harkokin waje, Bianca Ojukwu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Yadda kyamar baki ke cutar da yan Najeriya

Ministar ta nuna damuwa kan kalaman tunzura jama’a da ayyukan wasu kungiyoyin masu kyamar baki, tana mai cewa hakan na barazana ga rayuka da dukiyoyin baki ‘yan Afirka.

Kara karanta wannan

Jakadanci: Fani Kayode ya faɗi dalilin neman Tinubu ya dauke shi daga turai zuwa Afirka

A cewarta, wasu yara ana yi musu ba’a a makarantu tare da umartar su su koma kasarsu, abin da ta ce na iya jawo matsalar kwakwalwa da damuwa.

Bianca ta bayyana cewa Bola Tinubu ya umurci ofisoshin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu su kafa cibiyoyin karbar koke-koke cikin gaggawa.

A gefe guda, masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa kakaba takunkumi ga kamfanonin Afirka ta Kudu kamar MTN da MultiChoice zai iya cutar da Najeriya kanta.

Sun bayyana cewa irin wadannan kamfanoni sun samar da dubban ayyukan yi tare da bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin Najeriya da bangaren sadarwa.

An tura jakadan Najeria a Afirka ta Kudu

Mun ba ku labarin cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya tabbatar da nadinsa a matsayin jakadan Najeriya zuwa Afirka ta Kudu.

Fani-Kayode wanda tsohon 'dan PDP ne ya ce hakan ya faru ne bayan amincewar Bola Tinubu saboda korafin da ya yi ga shugaban kasa.

Ya ce shi ne ya nemi a mayar da shi Afirka ta Kudu zuwa Jamus saboda ra'ayinsa na ɗan Afirka da kusancin manufofin ƙasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.