Lalata da masu neman fasfoti: Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da ma'aikaci

Lalata da masu neman fasfoti: Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da ma'aikaci

- An dakatar da wani ma'aikacin ofishin jakadancin Najeriya na kasar Jamus

- Ana zargin mutumin da yunkurin yin lalata da wata mata don gaggauta samar mata da fasfoti

- Jakadan Najeriya na kasar, ya ce ba za su lamunci rashin daraja da dibar albarka ba a aikinsu

Wani bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, na wani ma'aikacin ofishin jakadancin Najeriya na kasar Jamus, wanda aka gan shi yana tattauna yadda zai hadu da wata mata a otal yayi lalata da ita don yayi gaggawar samar mata da fasfoti.

A wata takarda ta ranar Talata, ofishin jakadancin sun dakatar da shi don su tabbatar da gaskiyar zargin da ake yi masa na lalata da sauran laifuka, The Cable ta wallafa.

Yusuf Tuggar, Ambasadan Najeriya a kasar Jamus, ya ce tabbas mutumin zai fuskanci fushin hukuma matukar aka kama shi da laifukan da ake zarginsa da su.

A cewar Tuggar, "Ba za mu amince da lalata da rashin daraja ba a aikinmu. Muna kokarin ganin mun yi bincike kwarai a kan lamarin da sauran laifuka na dibar albarka da za a iya ganowa a kansa."

KU KARANTA: Gwamnan Kogi ya ziyarci Buhari, ya mika wata muhimmiyar bukatar jiharsa gabansa

Lalata da masu neman fasfoti: Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da ma'aikaci
Lalata da masu neman fasfoti: Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da ma'aikaci. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai

A wani labari na daban, gwamnonin kudu-kudu sun bukaci fadar shugaban kasa ta ba su hakuri bayan ta fasa yin wani taron masu ruwa da tsaki da ya kamata a yi a Port Harcourt, Channels TV ta wallafa.

Kamar yadda wata takarda tazo daga gwamnatin jihar Rivers, gwamnatin tarayya ta shirya wani taron gwamnoni a ranar Talata, da sauran shugabannin yankin don tattauna matsalolin da kasa take fama da su, ciki har da matsalar zanga-zangar EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel