'A Kawo Dauki': Tashin Hankali da 'Yan Najeriya Suke ciki a Afrika ta Kudu
- 'Yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin kare su daga hare-haren ƙyamar baki
- Hukumar NiDCOM ta ba wa 'yan Najeriya shawarar rufe shagunansu tsakanin 27 zuwa 29 ga watan Afrilu domin kauce wa hare-hare a lardin Gauteng
- Yayin da Najeriya ta ba da shawarar ɓuya kawai, ƙasar Ghana ta ɗauki mataki mai tsauri a lokacin da aka ci zarafin wani dan kasarta a Afrika ta Kudu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Afirka Ta Kudu – Shugaban ƙungiyar ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu (NICASA), Rev. Frank Onyekwelu, ya nuna fargaba kan yadda ake ƙara mayar da ƙyamar baki a matsayin wani abu na yau da kullum a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Onyekwelu ya yi Allah-wadai da yadda wasu ƴan siyasa ke rura wutar ƙiyayya da kuma cin zarafin da wasu jami'an ƴan sanda ke yi wa ƴan Najeriya da sauran baƙi ƴan Afirka.

Source: Getty Images
Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Afrika ta Kudu
A halin yanzu, ana gudanar da zanga-zangar nuna ƙyamar baƙi a sassa daban-daban na ƙasar, inda masu zanga-zangar ke fasa shagunan baƙi tare da neman a kori duk wanda ba ɗan ƙasa ba, in ji rahoton Daily Trust.
Lardin Gauteng, wanda ya haɗa da biranen Johannesburg da Pretoria, shi ne ake sa ran zai fuskanci sababbin tarzoma tsakanin 27 zuwa 29 ga watan Afrilu.
Shugabar hukumar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri ta fitar da wata sanarwa a shafinta na X a ranar Juma'a kan halin da ake ciki.
An nemi 'yan Najeriya su rufe shaguna
Abike Dabiri ta bukaci ƴan Najeriya da su rufe shagunansu a ranar 27 ga watan Afrilu, wadda ita ce 'ranar 'yanci' a Afirka ta Kudu, har zuwa ranar 29 ga watan.

Kara karanta wannan
2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar
Sai dai wannan mataki ya fusata ƴan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta, inda suka soki gwamnatin tarayya kan abin da suka kira rashin ɗaukar mataki na zahiri.
A cewarsu, gaya wa mutane su rufe shaguna da ɓuya a gida ba shi ne mafita ba, domin hakan ba zai hana ɓata-gari lalata dukiyoyinsu ko neman su a inda suke ɓuye ba.
Karanta sanarwar shugabar NiDCOM a nan kasa:
Yadda Ghana ta dauki nata matakin

Source: Getty Images
Yayin da ake sukar matakin Najeriya, ƙasar Ghana ta nuna wa duniya yadda ake kare ɗan ƙasa. Bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna ana cin zarafin ɗan ƙasarta mai suna Emmanuel Asamoa, gwamnatin Ghana ta kira babban jami'in diflomasiyyar Afirka ta Kudu a Accra domin nuna bacin ranta.
Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Ablakwa, ya sanar da cewa gwamnati za ta dauke Asamoa daga Afirka ta Kudu tare da biyan dukkan kuɗaɗen tafiyarsa, in ji rahoton BBC.
Matakin na Ghana ya tilasta wa hukumomin Afirka ta Kudu neman afuwa a hukumance tare da gudanar da taron diflomasiyya na gaggawa, lamarin da ya sa ƴan Najeriya ke kiran gwamnatinsu da ta koyi darasi daga wannan tsayin daka.
An kona dan Najeriya a Afrika ta Kudu
A wani rahoto, Legit Hausa ta ruwaito cewa, an kona wani dan Najeriya har lahira a Rustenburg dake South Africa bayan wasu 'yan ta'adda sun cinna wa motarsa wuta.
Hukumar ‘yan sandan Afrika ta Kudu ba su yadda cewa hakan nada alaka da rikicin zanga-zangar nuna kyamar baki da ake ci gaba da yi a kasar ba
Motoci biyu aka sawa wuta a warare daban daban, wanda wasu ‘yan ta’adda da ba’a san ko suwanene ba sukayi a rahotanni da aka samu.
Asali: Legit.ng

