Sojoji Sun Yi Dabara Sun Cafke 'Dan Bindiga Kachalla Halilu da Ya Shiga Kasuwa tsakar Rana

Sojoji Sun Yi Dabara Sun Cafke 'Dan Bindiga Kachalla Halilu da Ya Shiga Kasuwa tsakar Rana

  • Dakarun Najeriya sun dauki matakin gaggawa kan wani dan bindiga bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 4 ga Yunin 2026 a Zamfara
  • Bayanan sirrin da aka samu sun nuna cewa an hango wani dan bindiga mai suna Kachalla Halilu da ake nema ido rufe a kasuwa a jihar Zamfara
  • A cewar majiyoyin tsaro, dakarun sun yi gaggawar tura jami’ansu zuwa wurin tare da samun nasarar kama wanda ake zargin ba tare da wata matsala ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kama wani da ake zargi da kasancewa jagoran ‘yan ta’adda mai suna Kachalla Halilu a wani samame da suka gudanar bisa bayanan sirri.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kama Kachalla Halilu ne a kasuwar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Musulmai sun soki yan bindiga da suka bukaci shari'ar Musulunci a madadin fansa

Taswirar jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Zagazola Makama, mai kafar yada labarai da ta fi mayar da hankali kan yaki da masu tayar da kayar baya, ya wallafa cewa dakarun Bataliya ta 8 ne suka gudanar da aikin bayan samun sahihan bayanan sirri.

Yadda aka kama Kachalla Halilu

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sun tura jami’ansu zuwa kasuwar Shinkafi bayan hango Kachalla Halilu tare da kama shi ba tare da ya nuna wata turjiya ba.

Ita The Cable ta rahoto cewa kayayyakin da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da babur, wayar hannu, hula da kuma magungunan dabbobi.

“Dakarun sun dauki mataki cikin gaggawa bayan samun rahoton sirri kuma sun yi nasarar kama wanda ake zargin yayin aikin,”

In ji majiyoyin.

A cewar rahotanni, an mika wanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato ga jami’an leken asirin soji domin ci gaba da bincike.

Sojoji na kara kokari a Zamfara

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi

An ce kamen wani bangare ne na ci gaba da ayyukan soji da ke da nufin tarwatsa kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu aikata laifuffuka da ke aiki a Zamfara da sauran sassan yankin Arewa maso Yamma.

Jami’an tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin gano irin rawar da wanda ake zargin ya taka na ayyuka marasa kyau da kuma gano masu hada baki da shi.

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu sojojin Najeriya a fagen yaki da 'yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi fama da ‘yan bindiga da sauran munanan laifuffuka, yayin da jami’an tsaro ke kara kaimi wajen gudanar da ayyuka kan kungiyoyin masu dauke da makamai da ke aiki a yankin.

‘Yan bindiga sun kai hari a Abuja

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu masu dauke da makamai sun kashe wani dan banga tare da yin garkuwa da wasu mutum hudu a yankin Kubwa da ke Abuja.

Mazauna yankin da abin ya faru sun ce kusan mahara 28 ne suka kai harin da sanyin safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin shekarar 2026.

Jami’an tsaron hadin gwiwa sun fara aikin bincike domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da neman maharan da suka shiga daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng