Musulmi Sun Soki Yan Bindiga da Suka Bukaci Shari’ar Musulunci a Madadin Fansa
- Wata kungiyar Musulmi ta yi Allah-wadai da masu garkuwa da mutane da suka bukaci sai an kafa shari'ar Musulunci saboda bukatunsu
- Kungiyar ta caccaki maharan tana mai cewa ba sa wakiltar Musulunci ko Musulmai ko ta wani hanya saboda laifuffukansu
- Bayan sace dalibai 39 da malamai bakwai tare da kashe mutum biyu a Oriire, kungiyar ta jaddada cewa Musulunci ya haramta ta’addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Kungiyar Musulmin Oyo ta yi kakkausar suka kan bukatun da masu garkuwa da mutane suka danganta da Shari’a.
Kungiyar ta bayyana cewa ‘yan ta’adda ba sa wakiltar koyarwar Musulunci kuma ba za su iya magana a madadin Musulmai ba.

Source: Facebook
Shugabannin kungiyar sun bayyana haka ne a bayan masu garkuwa da mutane sun yi kokarin kare ayyukansu ta hanyar amfani da addini, cewar Tribune.
Yadda yan bindiga suka sace dalibai, malamai
Legit Hausa ta ruwaito cewa akalla dalibai 39 da malamai bakwai aka sace, yayin da mutum biyu suka rasa rayukansu yayin harin yan bindiga.
Yan ta’adda sun kai hari makarantu uku a kauyukan Ahoro-Esiele da Yawota da ke karamar hukumar Oriire a ranar 16 ga Mayun 2026.
Musulmi sun soki dabarar yan bindiga
Da take mayar da martani kan abubuwan da suka biyo bayan kokarin gwamnati na ceto wadanda aka sace, musamman sharudan da aka ce masu garkuwar sun gindaya.
Kungiyar ta bayyana cewa Musulunci ya haramta satar mutane, ta’addanci da kuma karbar kudin fansa daga marasa laifi.
Ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Alhaji Ishaq Kunle Sanni, da babban sakatarenta, Alhaji Murisiku Abidemi Siyanbade suka sanya wa hannu.

Source: Original
Abin shari'ar Musulunci ke koyarwa
Sanarwar ta ce sahihiyar Shari’a tana koyar da adalci, zaman lafiya da kare rayuwar dan Adam, abubuwan da suka saba kai tsaye da ayyukan masu aikata laifuffuka, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi
Kungiyar Musulmi a Oyo ta sake bayyana cikakken goyon bayanta ga jami’an tsaro tare da yin kira ga hukumomi su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Ta yi nuni da ayar Alkur’ani mai tsarki daga sura ta biyar aya ta 32, wadda ta bayyana cewa duk wanda ya kashe rai ba tare da hakki ba kamar ya kashe daukacin bil’adama ne, sannan wanda ya ceci rai kamar ya ceci daukacin mutane ne.
Sanarwar ta kuma bukaci Musulmai da sauran mazauna Oyo su kasance cikin lura, su rika kai rahoton duk wani motsi da ake zargi, tare da kin amincewa da duk wani yunkuri na karkatar da koyarwar Musulunci mai cike da zaman lafiya.
Gwamnatin Oyo ta karyata rahoton ceto dalibai
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Oyo ta ce bidiyon da ke yawo na cewa an sako dalibai da malamai da aka sace a Oriire karya ne.
Kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, Dotun Oyelade, ya ce har yanzu ana kokarin ceto wadanda aka sace.
Gwamnati ta bukaci jama'a su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su, yana cewa babu dalibin da aka sako zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng
