Akwai Matsala: Abubuwa 4 da 'Yan Ta'adda Suka Nema kafin Su Sako Dalibai da Malaman Oyo
- 'Yan bindigar da suka sace dalibai a makarantu uku a jihar Oyo sun gindaya sharudda hudu kafin sako duka mutanen da ke hannunsu
- Daga cikin sharuddan da aka ce sun kafa har da sakin wasu manyan jagororin kungiyar Ansaru da ke tsare a hannun jami'an tsaro
- Gwamnatin Oyo ta ki cewa komai kan abubuwan da masu garkuwar suka nema, ta ce fadin halin da ake ciki zai iya kawo cikas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’adda da ke rike da malamai da daliban da aka sace daga makarantu uku a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo sun gabatar da sharuɗɗa guda huɗu.
An kai farmaki a makarantu da ke Esinele, Yawota da Alawusa a ranar 15 ga watan Mayu, inda aka sace dalibai da malamai da dama.

Kara karanta wannan
Satar dalibai: Hanyoyi 6 da makarantu za su bi su kare kansu daga 'yan bindiga a Najeriya

Source: Original
Abubuwa 4 da masu garkuwa suka nema
Jaridar Punch ta tattaro cewa masu garkuwar sun ce dole ne a cika wasu bukatu kafin su saki wadanda ke hannunsu.
Daga cikin sharuddan da yan ta'addan suka kafa har da sakin wasu shugabanninsu da ake tsare da su, biyan kudin fansa, samar da motoci kirar Hilux guda biyu, da kuma aiwatar da dokokin Shari’a a wasu fannoni.
'Yan ta'adda sun nemi sakin shugabannin Ansaru
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda ake neman a sako akwai Mahmud Usman (wanda aka fi sani da Abu Bara’a ko Abbas Mukhtar) da mataimakinsa Abubakar Abba (wanda aka fi sani da Isah Adam ko Mahmud Al-Nigeri).
Wadannan mutanen su ne shugabannin kungiyar Jama’atu Ansarul Muslimeena Fii Bilaadis Sudan (JAMBS), wacce aka fi sani da Ansaru, wata kungiyar da ta balle daga Boko Haram.
An zarge su da hannu a ayyukan ta’addanci tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015, tare da alakanta su da fashin gidan yarin Kuje da aka yi a 2022.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
Yadda aka gurfanar da jagororin Ansarun
Rahotanni sun ce an kama su tsakanin watan Mayu zuwa Yuli 2025, kuma suna fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Mahmud Usman ya amsa laifi daya na hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, inda ya bayyana cewa yana amfani da kudin wajen sayen makamai da daukar nauyin ayyukan garkuwa da mutane.
Sai dai ya musanta wasu tuhume-tuhume 31 da ake yi masa, yayin da yake tsare a hannun DSS, kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.
Shi ma mataimakinsa, Abba, ya musanta dukkan tuhume-tuhume 32 da ake masa, kuma shari’arsa na ci gaba a kotu.

Source: Facebook
Matsayar gwamnatin jihar Oyo
Rahotanni sun ce masu garkuwar na neman kudin fansa har Naira biliyan daya (₦1bn), wanda za a tura zuwa asusun banki a Jamhuriyar Benin, duk da cewa ba a tabbatar da sahihancin wannan adadi ba.
Gwamnatin Oyo ta ce ba za ta yi tsokaci kan sharuɗɗan ko yadda ake tattaunawa ba, Kwamishinan Yada Labarai, Dotun Oyelade, ya ce bayyana dabarun gwamnati zai iya kawo cikas ga kokarin ceto wadanda aka sace.
'Yan bindiga sun sako daliban Oyo?
A baya, kun ji cewa Gwamnatin jihar Oyo ta musanta wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa dalibai da malami da aka sace sun kubuta.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama'a na jihar, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana cewa rahoton ba gaskiya ba ne.
Oyelade ya jaddada cewa sabanin abin da ake yadawa a shafukan sada zumunta, har yanzu wadanda aka yi garkuwa da su ba su dawo gida ba
Asali: Legit.ng
