Abin Tausayi: 'Yan Bindiga Sun Bude wa Mutane Wuta bayan Kammala Sallar Juma'a
- 'Yan bindiga sun bude wa mutane wuta suna tsakiyar hutawa bayan Sallar Juma'a a yankin karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe akalla mutane 16, yayin da wasu da dama suka gudu suka bar gidajensu
- Rundunar 'yan sandan reshen jihar Katsina ta bayyana cewa ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba zuwa yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Akalla mutane 16 ake zargin sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka bace bayan wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai kauyen Kiliya da ke kusa da Bagagadi a karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa harin ya faru ne ranar Juma’a jim kadan bayan mazauna kauyen sun kammala sallar Juma’a.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun far wa bayin Allah bayan sun dawo daga masallaci sun zauna suna hira da tattaunawa cikin yanayin shagulgulan Babbar Sallah.
Yadda yan bindiga suka far wa mutane
Wani mazaunin yankin ya ce ya fara hango wasu ‘yan bindiga biyu dauke da bindigogi suna tafe a kan babur.
Ya ce:
"Bayan mun gama sallar Juma’a muna zaune tare da sauran mutanen kauye. Na kira wani yaro mai sayar da kunu na sayi kwano guda daga gare shi lokacin da ‘yan bindigar suka iso.
"Na ga mutum biyu ne a kan babur. Mutane suka fara gudu, su kuma suka ce kada mu gudu, amma ba zato ba tsammani suka fara harbi.
"Ni da wannan yaron muka gudu mu ka shiga wani gida mu ka buya. Muna ciki muna jin ihun mutane da karar bindiga a ko’ina. Bayan wani lokaci harbin ya tsaya.
"Da muka fito muka tarar da gawarwaki kusan 16 kwance, ciki har da wasu daga cikin ‘yan uwana."
Mutane sun tsere daga kauyen
Majiyar ta kara da cewa bayan harin, fiye da mutane 400 sun tsere zuwa kauyen Bagagadi domin neman mafaka, yayin da wasu da dama suka koma kauyen Radda saboda tsoron sake kai hari.

Kara karanta wannan
Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri
Hakazalika, wani mazaunin kauyen Bagagadi ya ce sama da mutum 30 daga kauyen Kiliya, mafi yawansu mata da yara, suna samun mafaka a gidansa bayan harin, cewar rahoton Vanguard.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa harin na iya kasancewa ramuwar gayya, saboda kwanaki kadan kafin hakan, wasu mazauna yankin sun kashe wasu mutum biyu da ake zargi ‘yan bindiga ne.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce har zuwa lokacin tattaunawar ba su samu rahoton harin a hukumance ba.
Wani jami'in C-Watch da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Legit Hausa cewa ya kamata a jingine batun sulhu da yan bindigar nan, a yake su da yaren da suke fahimta.
"Kwanakin baya mutanen nan suka shiga kauyuka 2 a Bakori suka kashe mutane, kuma a haka anyi sulhu da su a karamar hukumar, ina matsayar yarjejeniyar da aka yi?
"Tun farko ba na goyon bayan wannan sulhu, kamata ya yi a tunkare su da yaren da suke fahimta, ya kamata mutane su cire tsoro, su yi fito na fito da wadannan miyagu," in ji shi.
Mahara sun kashe mutum 11 a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun far wa mutanen kauyuka biyu bayan sun daga kasuwa a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Harin ya faru ne da tsakar rana a ƙauyukan Gidan Wawu da Gidan Sarkin Noma, waɗanda maƙwabtan juna ne a karkashin gundumar Guga.
A cewar mazauna garin, maharan sun kashe mutane 11, sun ƙona gidaje, sun lalata kayayyaki, sannan sun kwashe dabbobi kafin su tsere daga yankin
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

