Farashin Danyen Mai Ya Ruguzo bayan Trump Ya Hana Isra'ila kai Hari Lebanon

Farashin Danyen Mai Ya Ruguzo bayan Trump Ya Hana Isra'ila kai Hari Lebanon

  • Farashin makamashi ya ragu sakamakon sassaucin rikicin Gabas ta Tsakiya bayan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da suka shafi Lebanon
  • Farashin danyen mai samfurin Brent, bayan ya haura dala 97 kan kowace ganga, ya sauka ƙasa da dala 95 yayin da farashin West Texas ya ragu zuwa dala 91.9
  • Ana sa ran cewa farashin man zai kara sauka kasa sosai idan aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da za ta kawo karshen yakin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Farashin danyen mai ya ragu da kusan dala 3 a ranar Alhamis yayin da masu zuba jari suka yi hasashen cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya raguwa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da samun haske kam tsayar da hare-haren Isra'ila a Lebanon wanda daga ƙarshe zai iya kaiwa ga sake buɗe mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi

Mutane na sayen man fetur a gidan mai
Mutane sun taru a gidan mai za su saye fetur a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar Reuters, saukar farashin ya biyo bayan sanarwar da Isra’ila da Lebanon suka yi cewa sun amince da aiwatar da tsagaita wuta, lamarin da ya ƙara karfafa yiwuwar samun ci gaban diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran.

Rahotanni sun ce Iran ta sanya kawo ƙarshen rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah, ƙungiyar da ke da alaƙa da Iran a Lebanon, a matsayin ɗaya daga cikin sharuɗan cimma duk wata yarjejeniya.

Farashin mai ya sauka a duniya

Rahotanni sun nuna cewa farashin mai na Brent ya ragu da dala 3.20 (3.27%) zuwa dala 94.61 kan kowace ganga a ranar Alhamis.

A daya bangaren kuma, farashin mai samfurin US West Texas Intermediate ya ragu da dala 3.71 (3.86%) zuwa dala 92.31 kan kowace ganga.

Farashin ya ƙaru da kusan kashi 2 cikin 100 a ranar Laraba sakamakon sababbin tashin hankula a Gabas ta Tsakiya, ciki har da rahotannin hare-haren Iran a Kuwait da kuma hare-haren sojojin Amurka kusa da mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Gaddafi: Yadda makamai suka shiga hannun 'yan ta'addan Najeriya daga Libya

Yadda ake fatan yakin zai lafa

Anadolu Agency ta ruwaito cewa a Amurka, majalisar wakilai mai rinjayen jam’iyyar Republican ta amince da wani ƙuduri a ranar Laraba da ke da nufin hana Shugaba Donald Trump ci gaba da ɗaukar matakin soja kan Iran.

Sai dai har yanzu matakin na buƙatar amincewar majalisar dattawa da kuma rinjayen kashi 2 bisa 3 a majalisun biyu domin soke duk wata yiwuwar amfani da ikon da Trump ke da shi.

A halin da ake ciki, jami'in gwamnatin Rasha Alexander Novak ya ce samar da mai a Rasha ya ragu tun farkon shekarar nan saboda gyaran matatun mai da ba a tsara ba, wanda shi ne karo na farko da wani jami’in Rasha ya amince da wannan raguwa.

A Amurka kuma, rumbun ajiyar ɗanyen mai ya ragu sosai. Bayanai daga hukumar kula da bayanai kan makamashi sun nuna cewa man ya ragu da ganga miliyan 8.

Matatar Dangote a Legas
Wani sashe na matatar Dangote da ke Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

'Yan kasuwar mai sun ce haɗuwar raguwar fargabar siyasa da sauye-sauyen bayanan samar da mai na ci gaba da haifar da sauyin farashi a kasuwannin ɗanyen mai na duniya.

Kara karanta wannan

An samu hirar Trump da jami'ansa da ke nuna fargabar yaki da Iran

A Najeriya kuwa, kamfanin NNPCL ya samu ƙarin sama da 70%. Haka kuma matatar Dangote ta amfana daga yawaitar fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje, amma talakawa na ci gaba da fama da hauhawar farashin mai.

Amfanin cire tallafin mai a Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sake magana kan cire tallafin man fetur da ya yi a 2023.

Bola Tinubu ya ce cire tallafin mai ne ya hana Najeriya fadawa cikin babbar matsalar tattalin arziki da durkushewa, inda ya ce ya jinjina wa jama'ar kasar.

Shugaban ya yabawa gwamnoni bisa yadda ya ce sun taka muhimmiyar rawa wajen kawo cigaba a shekara uku da ya yi suna aiki tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng