Isra'ila Ta Yi Ikirarin Hallaka Kwamandan Hezbollah ana Kokarin Tsagaita Wuta a Lebanon
- Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe babban injiniyan Hezbollah a wani hari da suka kai a Lebanon makon da ya gabata duk da maganar sulhu
- Rahotanni sun nuna wasu ministocin Gwamnatin Isra’ila ba su gamsu da yarjejeniyar tsagaita wuta da ake ƙoƙarin sabuntawa ba
- Hare-haren Isra’ila a birnin Tyre na Kudancin Lebanon sun yi sanadin mutuwar mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Lebanon — Rundunar Sojin Isra’ila (IDF) ta sanar a ranar Juma’a, 5 ga watan Yuni, 2026 cewa wani hari da ta kai a Lebanon a makon da ya gabata ya yi sanadin mutuwar babban injiniyan ƙungiyar Hezbollah.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ke shiga tsakani domin tabbatar da ita tsakanin ɓangarorin biyu.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo

Source: Getty Images
Kafar Aljazeera ta ruwaito cewa wasu daga cikin ministoci a Gwamnatin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, sun nuna rashin gamsuwa da sabon yunƙurin sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin jami'an gwamnayin sun nemi a gabatar da batun a gaban majalisar ministoci domin kada kuri’a kafin amincewa da ita.
Benjamin Netanyahu ya ce babu yarjejeniya tukuna
Times of Israel ta wallafa cewa ministocin sun soki yarjejeniyar da suka bayyana a matsayin mai rauni a yayin taron majalisar ministoci da aka gudanar a daren Alhamis.
An ce wakilan Isra’ila da Lebanon sun amince da sabunta tattaunawar tsagaita wuta a wani taro da aka gudanar a birnin Washington.
Sai dai Netanyahu ya ƙi amincewa da bukatar kada kuri’a kan batun, yana mai cewa har yanzu babu wata yarjejeniya da aka kammala saboda Hezbollah ba ta amince da sharuddan da aka gindaya ba.
Rahoton ya ce firaministan ya shaida wa ministocin cewa ba zai yanke hukunci kan yarjejeniyar ba muddin Hezbollah ba ta nuna amincewa da ita ba.
Hezbollah ta ci gaba da adawa
Shugaban Hezbollah, Naim Qassem, ya bayyana a ranar Alhamis 4, ga watan Yuni, 2026 cewa ƙungiyarsa ba za ta dakatar da kai hare-hare a Arewacin Isra’ila ba ana ci gaba da kai hare-hare a cikin Lebanon.
Kalaman nasa sun nuna cewa har yanzu akwai babban gibi tsakanin ɓangarorin biyu duk da ƙoƙarin da ake yi na cimma tsagaita wuta ta hanyar shiga tsakani daga ƙasashen waje.

Source: Facebook
A gefe guda kuma, wasu hare-haren Isra’ila da aka kai a daren Juma’a, 5 ga watan Yuni, 2026 a birnin Tyre da ke Kudancin Lebanon sun yi sanadin mutuwar mutum bakwai.
Majiyar ta ce hari ɗaya da aka kai kusa da wani asibiti ya kashe mutum huɗu tare da jikkata bakwai, sannan ya haddasa ƙananan ɓarna ga ginin asibitin.
Trump ya caccaki Firaministan Isra'ila
A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya kalamai masu kaushi kan Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ya yi kalaman kan Netanyahu saboda yakin da yake yi a Lebanon duk da kiran da ake yi masa na dakatar da aikin soji a sassan kasar.
Shugaba Trump ya dankaro waɗannan munanan kalaman zagi ne saboda barazanar da Isra'ila ke yi na jefa bama-bamai a babban birnin Lebanon, wato Beirut ganin zai iya kawo cikas.
Asali: Legit.ng

