Gaddafi: Yadda Makamai Suka Shiga Hannun 'Yan Ta'addan Najeriya daga Libya

Gaddafi: Yadda Makamai Suka Shiga Hannun 'Yan Ta'addan Najeriya daga Libya

  • Majalisar dinkin duniya ta ce wasu makamai da aka wawure a rikicin Libya na shekarar 2011 sun koma hannun ƙungiyoyin 'yan ta'adda a Najeriya
  • Wakiliyar majalisar kan harkokin makamai ce ta bayyana hakan a New York yayin tattaunawa kan barazanar yaduwar makamai a fadin duniya
  • Jami’ar ta nuna nadama cewa makamai na ci gaba da haifar da tashin hankali a cikin al’umma ko da bayan yaƙe-yaƙe da aka saye su domin su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dinkin duniya ta ce wasu makamai da aka yi amfani da su a rikicin Libya na 2011 sun shiga hannun ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a Najeriya.

Mataimakiyar shugaban majalisar Izumi Nakamitsu ce ta bayyana hakan a hedikwatar majalisar dinkin duniya da ke New York, Amurka.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Sojoji sun hallaka kwamandojin ƴan ta'adda, mayaka 50

Izumi Nakamitsu a wajen taro
Izumi Nakamitsu na bayani a taro majalisar dinkin duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Punch ya nuna cewa Izumi Nakamitsu ta fadi haka ne a ranar Talata yayin da wakilai ke tattaunawa kan yaduwar makamai ba bisa ƙa’ida ba a duniya.

Makaman Libya sun zo Najeriya

Nakamitsu ta bayyana Libya a matsayin misali, inda makaman da suka watsu a lokacin da bayan rikicin 2011 da ya kawo ƙarshen mulkin Muammar Gaddafi suka bazu a yankin Sahel, ciki har da Nijar, Burkina Faso da Najeriya.

“Wasu daga cikinsu daga baya sun shiga hannun ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi, abin da ke nuna yadda makaman rikici guda ɗaya za su iya dagula zaman lafiya a ƙasashe makwabta bayan shekaru,”

In ji ta.

“Ƙarshen rikici ba yana nufin ƙarshen yaduwar waɗannan makamai ba; suna ci gaba da yawo kuma suna ci gaba da cutar da mutane.”

A wasu sassan Afirka, majalisar dinkin duniya ta ce yawaitar ƙananan makamai na iya rushe ƙoƙarin gina zaman lafiya ko da bayan rikici ya lafa.

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta shiga maganar tsare Nnamdi Kanu a Najeriya

Marigayi Muammar Gaddafi
Muammar Gaddafi a taron majalisar dinkin duniya. Hoto: Getty Images
Source: Instagram

Illar yaduwar makamai a duniya

A cewar Nakamitsu, makamai ba bisa ƙa’ida ba na da alaƙa da take haƙƙin ɗan Adam, ta’addanci da kuma cin zarafin mata a duniya.

“Ba batun tsaro kaɗai ba ne. Batun gina zaman lafiya ne, batun haƙƙin ɗan Adam ne, kuma batun ci gaba ne,”

In ji Nakamitsu.

Ta ce shekaru bayan an manta da rikicin Libya, makaman da aka yi amfani da su wajen yaƙe-yaƙen na ci gaba da yawo, suna ƙetare iyakoki, suna ƙara jawo rusa zaman lafiya.

Tribune ta wallafa cewa ta ce:

“Yaƙe-yaƙe sun ƙare, amma abin takaici, makaman da aka yi amfani da su a wannan rikici ba sa ƙarƙashin cikakken iko,”

Buratai ya yi magana kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa tsohon hafsun sojan kasan Najeriya, Tukur Buratai ya yi magana kan yaki da 'yan ta'adda da samar da tsaro a Najeriya.

Ya ce cewa yana da muhimmanci a kara yawan jami'an tsaro, inganta rayuwarsu, samar da alaka mai kyau da al'ummomi idan ana so a yi nasara.

Buratai ya yi magana ne yayin da ya ke tsokaci kan yadda sace wasu dalibai a jihar Oyo ke cigaba da daukar hankali a Najeriya a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng