Matatar Dangote Ta Yi Rangwame a Farashin Litar Man Jiragen Sama a Najeriya
- Matatar Dangote ta rage farashin kowace litar man jiragen sama na Jet A1 daga N1,750 zuwa N1,650 a Najeriya
- Wannan rangwame na zuwa ne yayin da kamfanonin jiragen sama auna fara kokawa kan tsadar mai tare da barazanar dakatar da ayyukansu
- Ana sa ran rage farashin zai taimaka wajen saukaka kudin sayen mai ga kamfanonin jiragen sama tare da daidaita harkokin zirga-zirga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Matatar Dangote da ke jihar Legas ta rage farashin man jiragen sama na Jet A1 daga N1,750 zuwa N1,650 kan kowace lita.
Matatar hamshakin attajirin, wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka ta yi haka ne domin rage wa kamfanonin jiragen sama nauyin kashe kudade tare da tabbatar da wadataccen mai a fadin kasa.

Source: UGC
Dangote ya rage farashin man jirgi
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito
Matatar ta ce ta kuma samar da damar bashi na kwanaki 30 ba tare da ruwa ba ga ‘yan kasuwa da kamfanonin jiragen sama, tare da kariyar garantin banki.
Haka zalika, ta kuma sanar da sauya tsarin sayar da man daga farashin Dala zuwa tsarin farashin Naira.
Kamfanonin jirage na fuskantar matsi
Wannan mataki na zuwa ne yayin da kamfanonin jiragen sama na cikin gida ke fama da tsadar gudanar da aiki, inda farashin man jiragen sama ke cin kaso mai yawa na kudaden su.
Masu ruwa da tsaki a bangaren sufurin jiragen sama sun dade suna nuna damuwa kan tashin farashin Jet A1, suna gargadin cewa hakan na jefa kamfanonin cikin matsin tattali tare da barazana ga ci gaba da zirga-zirgar jirage a Najeriya.
Ana sa ran rage farashin zai taimaka wajen saukaka kudin sayen mai ga kamfanonin jiragen sama, daidaita harkokin zirga-zirga tare da rage tsadar kudin tikitin jirage ga fasinjoji.
Dangote zai sayar wa mutane hannun jari
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfanin ya ki amincewa da yunkurin NNPCl na kara sayen hannun jari a matatar fiye da kaso 7.25 cikin 100 da take da shi yanzu.

Source: Getty Images
Ya ce an dauki matakin ne domin bai wa talakawan Najeriya damar mallakar hannun jari a matatar maimakon takaita shi ga wasu tsirarun masu zuba jari.
“Idan ka dubi matatar mu, kamfanin mai na kasa ya riga ya mallaki kaso 7.25 cikin 100 kuma suna kokarin kara saye amma mu muka ce a’a, muna son sauran jama'a su samu damar zama wani bangare na matatar,” in ji Dangote.
Matatar Dangote ta rage farashin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta janye ƙarin farashin fetur da ta yi a baya, inda ta mayar da farashin kowace lita na fetur zuwa N1,275.
Wani babban jami’i a matatar man Dangote, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da ƙarin farashin na farko amma ya ce matatar yanzu ta janye shi.
Ya bayyana cewa an ɗauki wannan shawarar cikin gaggawa ne sakamakon sauyin da aka samu, musamman faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Asali: Legit.ng


