Tinubu Ya Fadi Yadda Cire Tallafin Mai Ya Hana Najeriya Durkushewa
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi a 2023 ya ceci Najeriya daga fuskantar durkushewar tattalin arziki
- Ya fadi hakan ne yayin da yake karbar bakuncin gwamnonin da suka kai masa gaisuwar Sallah tare da taya shi murnar cika shekaru uku a kan mulki
- Wadanda suka halarci taron gaisuwar sallah ga shugaban kasar sun hada da gwamnonin jihohin Lagos, Nasarawa, Jigawa, Sokoto, Kebbi da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce cire tallafin man fetur a farkon mulkinsa ya kubutar da Najeriya daga kusantar durkushewar tattalin arziki.
Bugu da kari ya ce gyare-gyaren da suka kasance masu wahala sun fara haifar da amfanin da jihohi da ’yan kasa ke gani a kasa.

Source: Twitter
Bayanin cire tallafin man fetur
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa bidiyon da shugaban kasar ya yi bayani game da cire tallafin mai a shafinsa na X.
Shugaba Tinubu ya ce:
“Lamarin ya kasance mai wahala a lokacin, amma mun tsallake shi. Mun fuskanci kararraki da zarge-zarge. Mun tsallake su. Maimakon durkushewar tattalin arziki, Najeriya ta tsira. Tattalin arzikin ya farfado. Yana bunkasa. Noma na habaka,”
In ji shugaban kasar lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi a gidansa da ke Ikoyi a Lagos domin bikin Sallah da kuma cika shekaru uku a kan mulki.
Tinubu ya kafa hujjar cewa tsarin tallafin man fetur ya shafe shekaru yana cinye dimbin kudi wanda 'yan tsiraru ne kawai a ’yan Najeriya ke amfana da su, yayin da muhimman bangarori ke tashi a tutar babu.
Bola Tinubu ya ce gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a fannin abubuwan more rayuwa, noma, zuba jari na jin kai da sauransu sun fara dawo da amincewar masu zuba jari tare da inganta tattalin arziki.
Bola Tinubu ya yabi gwamnoni
Shugaban ya yaba da rawar da gwamnonin jihohi suka taka wajen tafiyar da tunanin jama’a a lokacin mafi wahalar gyare-gyaren, yana cewa
“Na yi farin ciki cewa gwamnoni ba su karbar bashi daga gwamnatin tarayya ko neman agaji ba tare da sanin yadda za su rayu ko biyan albashi ba.
"Kun lallashi jama’armu su yi hakuri su jure wadannan shekaru uku na gyare-gyare masu radadi, lokacin da muka sake tsara tattalin arziki. Yau, ana ganin amfaninsu.”

Source: Facebook
Ya kara da cewa:
“Tattalin arzikin ya farfado. Muhimman alamomin tattalin arziki suna tafiya da kyau. Ana ci gaba da gina hanyoyi da abubuwan more rayuwa; wadanda aka yi watsi da su an dawo da su.
“Bangaren gidaje yana samun ci gaba sosai. Noma zai sake habaka. Za mu cimma wadatar abinci idan muka yi amfani da filayen da ke hannunku a jihohinku yadda ya kamata.”.
Ga bayanin da Tinubu ya yi a kasa:
Atiku ya bukaci Tinubu ya sauka
A wani labarin, mun kawo muku cewa Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan yadda ’yan ta’adda ke ci gaba da yi wa jama’a barazana.
Yayin da ya jaddada cewa babban nauyin kowace gwamnati shi ne tabbatar da tsaro da walwalar jama’arta, Atiku ya bukaci shugaba Tinubu ya sauka daga mulki.
Ya ce shugaba Tinubu ba shi da wata hujjar da za ta sa ya ci gaba da zama a Aso Rock ko da na kwana daya alhali 'yan ta'adda na cin karen su babu babbaka.
Asali: Legit.ng


