Mutane Za Su Warwarsa, An Ci Gaba da Raba Kyautar N20,000 da Buhun Shinkafa a Kano
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NASENI ta tallafa wa mutane 1,200 a karamar hukumar Kabo ta jihar Kano
- Wadanda suka amfana sun samu murhun girki mai amfani da makamashi mai tsafta da na’urorin hasken rana
- Kowane mai cin gajiyar wannan shiri ya samu buhun shinkafa da N20,000 domin tallafa wa rayuwarsa ta yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Kula da Ababen More Rayuwa na Kimiyya da Injiniya ta Kasa (NASENI) ci gaba da tallafa wa mutane marasa karfi a kashi na uku a jihar Kano.
A wannan karon, NASENI ta tallafa wa mazauna 1,200 na karamar hukumar Kabo ta jihar Kano karkashin kashi na uku na shirin tallafin Sustainable Empowerment Programme.

Source: Twitter
Leadership ta rahoto cewa n kaddamar da shirin ne a Kabo a karshen mako, inda aka mayar da hankali kan samar da makamashi mai tsafta, koyar da sana’o’i, bunkasa harkokin kasuwanci da samar da hanyoyi dogaro da kai.
Yadda aka rabawa mutane N20,000 a Kano
A karkashin shirin, wadanda suka amfana sun samu murhun girki mai amfani da hsken rana da na’urorin samar da hasken rana a gidaje.
Baya ga kayan makamashi, an kuma ba su tallafin da ya kunshi buhun shinkafa guda da kuma N20,000 a matsayin kudin taimako.
Shugaban NASENI, Khalil Halilu, ya ce an tsara shirin ne domin tabbatar da cewa sauyin amfani da makamashi ya wuce matakin hasashen masana zuwa gidaje a Najeriya.
“A NASENI, mun yi imanin cewa sauyin makamashi bai kamata ya kasance abin da muke tattaunawa a taruka kawai ba. Dole ne ya isa gidajenmu, al’ummominmu da kuma jama’armu,” in ji shi.
Khalil Halilu ya ce amfani da fasahar girki zai rage dogaro da makamashin gargajiya, ya taimaka wajen dakile sare itatuwa da kuma rage illolin sauyin yanayi, cewar rahoton Daily Nigerian.
NASENI na aiwatar da shirye-shirye 40
Shugaban hukumar ya ce tallafin da aka bai wa gidajen da suka amfana zai taimaka musu wajen magance wasu bukatun gaggawa tare da samar da damar gudanar da kananan sana’o’i da inganta rayuwa.
Ya bayyana cewa NASENI na aiwatar da shirye-shiryen tallafi sama da 40 a sassan Najeriya, da nufin mayar da kimiyya, fasaha da injiniya zuwa hanyoyin magance matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Source: Twitter
Khalil Halilu ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da kayan da kudaden da aka ba su cikin hikima, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen inganta jin dadin gidaje da karfafa tattalin arzikin al’umma.
An bude shafin raba tallafin N50,000
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar SMEDAN ta sake bude shirin ba da tallafin N50,000 ga kananan 'yan kasuwa a Najeriya.
Sai dai akwai sharadi ga masu cin gajiyar shirin, inda SMEDAN ta bayyana cewa duk wanda ya samu tallafin dole ne ya dauki akalla mutum daya aiki.
Hukumar ta bayyana cewa wannan shirin ya bambanta da Presidential Conditional Grant Scheme, duk da cewa dukkansu na bayar da tallafin N50,000 ga kananan sana'o'i.
Asali: Legit.ng

