Matatar Dangote Ta Kafa Tarihi, An Fara Tace Gangar Mai Sama da 650,000 a Rana

Matatar Dangote Ta Kafa Tarihi, An Fara Tace Gangar Mai Sama da 650,000 a Rana

  • Matatar Dangote ta ƙara ƙarfin tace ɗanyen mai zuwa ganga fiye da matakin da aka assasa ta a kai na tace ganga akalla 650,000 a kullum
  • Wannan na zuwa daga cikin wani shirin faɗaɗa ƙarfin matatar zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin watanni 30 masu zuwa
  • A yanzu, an gano iya karfin da matatar ta kai, wanda ake sa ran zai taimaka wajen wadata Najeriya, har da makwabtan kasashe da mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos — Matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa ta ƙara ƙarfin tace ɗanyen mai zuwa ganga 700,000 a rana.

Wannan na nufin tuni ta zarta matakin farko da aka dora matatar a kai na tace gangar danyen mai 650,000 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Ba sani ba sabo: Gwamnatin Kano ta gaji, an fara daukan mataki a kan 'yan daba

Matatar Dangote ta kara bunkasa
Shugaban rukunin kamanin Dangote a wata hira Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa matatar ta ce an cimma wannan nasara ne bayan gwajin aiki da masu ba da lasisin fasahar matatar suka gudanar, wanda ya tabbatar da ingancin aikinsu.

Matatar Dangote ta kara karfi

A ruwayar Daily Trust, matatar ta ce wannan ci gaba ya nuna cewa matatar na da damar sarrafa ƙarin ɗanyen mai tare da inganta yadda sassan samar da kayayyaki ke aiki.

Kamfanin ya ƙara da cewa nasarar ta ƙara tabbatar da matsayin matatar a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin tace mai a nahiyar Afrika.

Mataimakin shugaban sashen mai da iskar gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce ƙarin ƙarfin da aka samu wani ɓangare ne na shirin faɗaɗa matatar zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin watanni 30 masu zuwa.

Ana sa ran kara tace mai a matatar Dangote zai bunkasa samar da makamashi a Najeriya
Wani sashe na matatar Dangote da ke jihar Legas tare da ma'aikaci a kamfanin Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

A cewarsa, idan aka kammala wannan shiri, matatar za ta iya zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta haddasa asarar biliyoyin Daloli, ta lalata sansanonin Amurka 20

Edwin ya bayyana cewa faɗaɗawar za ta taimaka wajen ƙarfafa wadatar makamashi a Najeriya tare da rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.

Yadda matatar Dangote ke samar da mai

Tun a ranar 4 ga Fabrairu, 202 6 babban jami'in gudanarwa na matatar Dangote, David Bird, ya bayyana cewa matatar mai ƙarfin ganga 650,000 a rana za ta ƙara yawan tace mai zuwa ganga 700,000 nan gaba kaɗan.

Ya kuma bayyana cewa matatar na iya samar da fiye da lita miliyan 75 na man fetur a rana, yana mai cewa yanzu hankalin matatar ya fi karkata kan ƙara yawan kayayyakin da take samarwa.

A watan Oktoban 2025, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya sanar da shirin ƙara ƙarfin matatar daga ganga 650,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin shekaru uku.

NNPCL na jayayya da Dangote

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya zargi matatar Dangote da kokarin mallake kasuwar mai ta Najeriya ita kadai ba tare da barin wasu su samu dama ba.

Kara karanta wannan

Amurka ta ware N5bn don ba da kwangilar bibiyar cin zarafin addini a Najeriya

Kamfanin ya ce dakatar da lasisin shigo da mai zai iya haddasa karancin mai da tashin farashi a kasar nan yayin da Dangote ya maka shi a gaban kotu domin hana shi ba wasu lasisi.

Rikicin shari’ar na zuwa ne gabanin shirin matatar Dangote na sayar da hannun jari a watan Satumba, 2026 domin kara habaka samar da fetur a Afrika tare da kara fadada karfinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng