
Yan jihohi masu arzikin man fetur







Bayan taimakawa Nijar da tankokin mai, Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya ce Najeriya na cikin hadari kasancewar Nijar, Mali da Burkina Faso a mulkin soja.

Kungiyar dillalan mai ta PETROAN ta nemi a kafa doka da za ta kayyade sauya farashi zuwa sau daya cikin watanni shida domin hana rashin tabbas a kasuwa.

Gwamnatin tarayya ta amince da gina matatun mai uku da za su kara yawan gangar man da ake tace zuwa 140,000 a kullum, domin bunkasa samar da mai a Najeriya.

Wani masanin tattali a Najeriya ya bayyana cewa farashin man fetur zai cigaba da sauka a Najeriya har zuwa watan Yunin 2025 bayan Dangote da NNPCL sun rage kudi

Kamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin fetur daga ₦890 zuwa ₦825 kowace lita inda aka tabbatar da cewa a Lagos za a siyar da lita kan ₦860.

Kungiyar kasashe masu fitar da man fetur (OPEC) ta bayyana cewa Najeriya za ta iya rika fitar da gangar danyen mai akalla miliyan hudu a kullum saboda wasu dalilai.

Yayin da ake kokawa kan yawan haduran tankokin mai da ake samu, Hukumar NMDPRA ta haramta amfani da tankokin mai masu daukar lita 60,000 a hanyoyin Najeriya.

Fitaccen lauya a Najeriya, Femi Falana ya ce marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Yar’Adua ya soke sayar da matatar mai ta Port Harcourt saboda rashin bin ka'ida.

Kamfanin mai na kasa ya bayyana irin manyan nasarorin da ya samu ta fuskar farfado da matatun mai na Warri da Fatakwal, an fara gyaran ta Kaduna.
Yan jihohi masu arzikin man fetur
Samu kari