Yadda ake Cike Fom Din Neman Bashin Waya da Komfuta a Najeriya

Yadda ake Cike Fom Din Neman Bashin Waya da Komfuta a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta buɗe shafin neman bashin samun komfuta, wayoyin hannu da na'urorin zamani ga 'yan Najeriya
  • Shirin da ma'aikatun gwamnatin tarayya ke gudanarwa yana nufin bawa mutane damar biyan kudin na'urorin a hankali
  • A yanzu haka an fara shirin gwaji ne da wadanda suka shiga shirin 3MTT su 1,000 kafin a faɗaɗa shi zuwa ga sauran al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Sabon tsarin karbar bashin na'urorin zamani na gwamnatin tarayya, wato C.L.I.C.K.D., ya fara karɓar bayanai daga 'yan Najeriya da ke son samun komfuta, wayoyin hannu, da kwamfutar hannu (tablets) a kan farashi mai rahusa.

An kaddamar da shirin a ranar Talata, wanda CREDICORP ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar ma'aikatar sadarwa a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ricikin bayan zaben fitar da gwan ya raba kan APC a jihar Niger

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta ce an tsara C.L.I.C.K.D. ne domin taimaka wa 'yan Najeriya mallakar na'urorin zamani ta hanyar biya a hankali a maimakon biyan dukkan kudin a lokaci guda, inda aka fara da komfutocin da aka haɗa a gida Najeriya.

Yadda za a nemi bashin

  1. Za a ziyarci shafin credicorp.ng, wanda shi ne shafin hukuma na C.L.I.C.K.D.
  2. Latsa “Ina bukata”: Wannan zai kai ka tsaye zuwa fannin cika fom.
  3. Cika bayanan da ake buƙata:
    • Jihar zama: Zaɓi tsakanin jihohi 36 ko Babban Birnin Tarayya (FCT).
    • Bayani game da kai: Ma'aikaci mai karɓar albashi, mai zaman kansa, mai kasuwanci, ɗalibi, mai neman aiki ko ɗan NYSC.
    • Kudin shiganka na wata-wata: Ya tashi daga ƙasa da ₦100,000 zuwa sama da ₦1,000,000.
    • Shirin dabarun zamani: Za ka bayyana ko kana tsarin 3MTT, Learn2Earn da sauransu.
    • Na'urar da kake buƙata: Komfuta, wayar hannu, kwamfutar hannu ko wata daban.
    • Dalilin buƙatar na'urar: Za ka iya zaɓar dalilai da dama
    • A karshe za ka fadi yadda ka sami labarin C.L.I.C.K.D
  4. Tabbatarwa da amincewa: Kafin tura bayanan ka, dole ne ka amince da sharuɗan tabbatar da gaskiyar bayanan da kuma ba CREDICORP damar yin amfani da bayanan don tantance ka.
  5. Sai ka aika sokon ka

Kara karanta wannan

Manyan zarge zargen almundahanar kudi 5 da suka girgiza kamfanin NNPC

Su wane ne suka cancanta?

Shirin gwajin farko na komfutoci 1,000 ya tsaya ne kawai ga 'yan shirin 3MTT na Gwamnatin Tarayya, inda aka ƙaddamar da C.L.I.C.K.D. a matsayin shirin gwaji na ƙasa.

Nwagba ya bayyana cewa an fara rarraba na'urorin ne a Abuja inda mutane 77 suka rigaya suka karɓa, yayin da sauran komfutocin za a rarraba su ga 'yan shirin 3MTT na sauran jihohi a matakai daban-daban.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da Bola Tinubu ke yi wa 'yan Najeriya jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hukumar CREDICORP ba ta riga ta bayyana adadin kudin ruwa, tsawon lokacin biyan bashin, ko adadin kudin da za a fara biya na farko ba.

Tsarin noma na Renewed Hope

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da rarraba kayan tallafin noma a ƙarƙashin tsarin Renewed Hope.

Tsarin wanda Asusun Haɓaka Noma na Ƙasa (NADF) ke tafiyar da shi, wani muhimmin ɓangare ne na tsari ne na gwamnatin Tinubu.

Manoman za su amfana da rangwamen 75% na takin zamani, tare da mai da hankali kan noman masara, shinkafa, rogo, da waken soya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng