Aliko Dangote
Majalisar dokokin jihar Ogun ta bukaci shugabannin kamfanin Dangote da su bayyana gabanta domin amsa tambayoyi kan ayyukan kamfanin a yankin Ibese.
Kungiyar PETROAN ta ce farashin man fetur a matatar Fatakwal ya kai N1,045 wanda ya fi na Dangote tsada da. N75. Ana sa ran NNPCL zai daidaita farashin
Matatar man Alhaji Aliko Dangote ta rage farashin man fetur ga yan kasuwa domin saukaka musu daga N990 da ta sanar a farkon watan Nuwamba zuwa N970.
A wannan rahoton, za ku ji matatar Dangote ta fara duba yiwuwar fara sayo danyen man fetur daga kasar Amurka a kokarinta kara yawan fetur da ta ke tacewa a Najeriya.
Bayan yada jita-jitar mutuwar attajiri a Najeriya, Mike Adenuga, na kusa da shi kuma jigon PDP, Dele Momodu ya karyata labarin rasuwar mai kamfanin GLO.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka yana neman kudade yayin da yake shirin kawo karshen dogaron da kasar ke yi kan shigo da fetur daga kasashen waje.
An cimma matsaya tsakanin kungiyar dillalan man fetur na kasa (IPMAN) da matatar man fetur ta Dangote, an cimma yarjejeniyar samar da mai ga yan kasa.
Kungiyar ƴan kasuwa masu zaman kansu IPMAN ta sanar da cewa za a samu saukin akalla N50 a farashin kowace lita idan ta fara ɗauko mai daga matatar Ɗangote.
Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL ya ce tuni ya daina sayo tataccen man fetur daga ƙasashen ketare ya dawo kasuwanci da matatun mai na cikin gida a Najeriya.
Aliko Dangote
Samu kari