Kadarar Dangote Ta Doshi $100m, Fitaccen Ɗan Kasuwa zai Kafa Tarihi a Afrika
- Fitaccen attaijirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya ce kudin shigar da kamfaninsa ke samu na iya zarceDala biliyan 100 kafin shekarar 2030
- Ya bayyana matatar Dangote a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan masana’antu mafi girma a duniya da aka samar a jihar Legas da ke Najeriya
- Dangote ya ce kamfanin zai mallaki kusan 10% na karfin tace mai na Amurka, kuma idan sabon hasashensa ya tabbata,zai karya kundin tarihin kudi a Afrika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa na iya zarce hasashen samun kudin shiga na Dala biliyan 100 kafin shekarar 2030.
Idan wannan hasashe ya tabbata, lamarin da zai kafa sabon tarihi a nahiyar Afrika inda a karon farko, mutum daga shiyyar zai samu sama da $100m.

Source: Getty Images
Arise News ta wallafa cewa Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai bayan ya jagoranci manyan jami’an kamfanin rangadi a harabar matatar Dangote.
Matatar Dangote na kara habaka
Alhaji Aliko Dangote ya kara da bayyana cewa matukar kamfanin bai zarce Dala miliyan 100 ba, to a kai ga abin da aka saka a gaba ba.
Ya ce:
“Tambayar ita ce, na yi imani da yardar Allah, idan har muka tsaya a Dala biliyan 100 nan da shekarar 2030, to hakan yana nufin ba mu yi aiki tukuru ba. Ina ganin za mu wuce wannan adadi.”

Source: Getty Images
Ya kara da cewa:
“Idan mafi karancin abin da muka samu ya kasance Dala biliyan 100, hakan zai nuna cewa mun yi kokari, amma ba mu yi aiki sosai yadda ya kamata ba.”
Kamfanin Dangote zai kafa tarihi
Rahotanni sun nuna cewa idan har kamfanin Dangote ya kai wannan matsayi, zai zama karon farko da wani kamfani daga Afrika zai kai irin wannan girman kudin shiga.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa
A baya, manyan kamfanonin Afrika ba su taba wuce Dala biliyan 80 a kudin shiga ba, hatta a lokutan da kasuwar mai ta fi habaka.
Kamfanin makamashi na gwamnatin Aljeriya, Sonatrach, wanda ake dauka a matsayin mafi girman kamfani a AfRIka ta fuskar kudin shiga, ya taba samun sama da Dala biliyan 80 a shekarun da farashin mai ya yi tashin gwauron zabo.
Dangote ya alakanta wannan buri da fadada ayyukan matatar mai da sauran masana’antun kamfanin a fadin Afirka. Alhaji Aliko Dangote bayyana matatar Dangote a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan masana’antu mafi girma a duniya.
A cewarsa:
“Za mu mallaki kashi 10% na karfin tace mai na daukacin Amurka10%. Kuma za ta kasance matata mafi girma da aka taba ginawa a duniya. Don haka wannan ba karamin kasuwanci ba ne. Kasuwanci ne mai matukar girma.”
Dangote ya maka gwamnati a kotu
A baya, mun kawo labarin cewa matatar Dangote ta sake shigar da gwamnatin Najeriya kara a yunkurin naman soke lasisin shigo da mai da aka bai wa ‘yan kasuwa da kamfanin NNPCL.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kula da harkokin mai ta kasa ta NMDPRA a cikin 'yan kwanakin nan ta bai wa ‘yan kasuwa shida lasisin shigo da man fetur cikin Najeriya duk da akwai matatar Dangote.
Takardun kotu da manema labarai suka gani sun nuna cewa karar na neman soke lasisin shigo da mai da aka bai wa kamfanin mai na NNPC da wasu ‘yan kasuwar yayin da matatarsa ke ci gaba da aiki.
Asali: Legit.ng

