'Yan Bindiga Sun Shiga Abuja da Sassafe, Sun Kashe Mutane Sun Dauke Wasu
- Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari wani yanki na birnin tarayya Abuja, sun sace wani adadi na mutane sun tafi da su daji
- Wani shaidar gani da ido ya tabbatar wa manema labarai cewa maharan sun harbe wani dan banga da ke gadin wajen da suka kai farmakin
- Rahotanni sun nuna cewa an tura jami'an tsaro su bi diddigin barayin domin cafke su da ceto wadanda suka yi garkuwa da su a cikin dajin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An wayi gari da labarin wasu 'yan bindiga da suka kai wani mummunan farmaki wani sashe na birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan da ke dauke da makamai sun sace mutane tare da kashe wani dan banga da ke tsaron jama'a a yankin.

Kara karanta wannan
Abin ya yi muni: Sojan Najeriya da matasan NYSC 4 sun bakunci lahira a hanyar Adamawa

Source: Original
An sace mutum 4 a birnin Abuja
Punch ta ta wallafa cewa maharan sun sace mutane huɗu tare da kashe wani ɗan sa-kai a wani hari da suka kai yankin Byazhin da ke Kubwa, a ƙaramar hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Aliyu ya ce harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, yana mai cewa maharan suna ɗauke da manyan makamai.
Daily Post ta rahoto ya ce:
“Harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis. 'Yan bindigar sun kai kusan 28 da suka kai hari al’ummar yankin.
"Ina ganin watakila sun yi sansani a yankin kafin su kai harin. An yi awon gaba da mazauna yankin huɗu zuwa cikin daji yayin da aka harbi wani ɗan sa-kai da ke tsaron yankin, kuma ya mutu sakamakon harbin bindigar,”
In ji shi.
An yi jana'izar 'dan bangan
Wata majiyar tsaro da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce an riga an yi jana'izar ɗan sa-kan da aka kashe a sanadiyyar wannan mugun aiki.
Ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun fara aikin nema da ceto domin gano waɗanda aka sace:
“Gaskiya ne. An riga an yi jana’izar ɗan sa-kan. Sojoji da 'yan sanda da kuma 'yan sa-kai sun zo yankin. Sun riga sun shiga daji domin neman masu laifin da kuma ceto waɗanda aka sace,”

Source: Getty Images
'Yan sanda ba su ce komai ba
A halin da ake ciki, ƙoƙarin samun jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan Babban Birnin Tarayya, Josephine Adeh, bai yi nasara ba, domin kiran wayarta ya nuna ba a samun layin ba a lokacin da ake hada wannan rahoto.
Yankin Byazhin na Kubwa na ɗaya daga cikin yankunan da ke saurin bunƙasa a Babban Birnin Tarayya, kuma ya shahara da matsalolin tsaro da aka samu a baya-bayan nan.
'Dan majalisa ya ga sakaci a lamarin tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa wani dan majalisar wakilai ya yi zargin cewa shugabannin Najeriya na sakaci da matsalar tsaro.
A korafin da ya yi a zauren majalisar wakilai, dan majalisar ya ce suna haka ne lura da cewa matsalar bata shafar su ko iyalansu kai tsaye.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen samar da dabarun da za su tabbatar da cewa an samu cikakken tsaro a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

