Dubu Ta Cika: Matashin da Ya Kirkiri Muryar Tinubu Ta Bogi Ya Shiga Komar Ƴan Sanda
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wani matashi da ake zargi da ƙirƙirar muryar bogi ta amfani da fasahar AI tare da danganta ta ga Bola Tinubu
- Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce kama wanda ake zargin ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan yaɗuwar sautin
- Binciken kafafen yaɗa labarai ya nuna cewa VeryDarkMan bai wallafa sautin bogin ba, domin wani ne ya haɗa shi da bidiyonsa kafin ya yaɗa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi nasarar kama matashi da ake zargin ya ƙirƙiri muryar Bola Tinubu da fasahar AI.
Rundunar ta kama Ifechukwu Dennis saboda zargin ƙirƙirar sautin murya ta bogi da aka yaɗa a matsayin muryar Shugaba Bola Tinubu.

Source: Facebook
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da kama wanda ake zargin a ranar Alhamis ta shafinsa na X.
Muryar da ta karade kafofin sadarwa
A cewarsa, sashe na musamman na Sufeto Janar na ‘yan sanda ya kama Ifechukwu Dennis, wanda ya ƙirƙiri muryar bogin sannan ya yaɗa ta ga mutane a matsayin muryar Shugaba Tinubu.
Kamen ya kawo ƙarshen muhawarar da ta ɗauki kusan mako guda bayan wani bidiyo da ɗan gwagwarmayar sada zumunta, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya bazu a ranar 27 ga Mayu, 2026.
A cikin bidiyon, an ji wata murya mai kama da ta Shugaba Tinubu tana furta kalamai masu tayar da hankali, ciki har da zargin cewa rashin tsaro a Kudu maso Gabas da gangan ake yi.

Kara karanta wannan
Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci
An kuma ji muryar tana cewa ya matsa wa Peter Obi lamba ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2023, tare da nuna cewa bai damu da wahalhalun ‘yan Najeriya ba.

Source: Twitter
Bincike kan yada bidiyo daga VeryDarkMan
Sai dai binciken da kafafen yaɗa labarai daban-daban suka gudanar ya tabbatar da cewa VeryDarkMan bai wallafa sautin da aka yi wa kwaskwarima ba a asalin bidiyonsa.
An gano cewa wani mutum da ba a bayyana sunansa ba ne ya cire wani ɓangare daga bidiyon na VeryDarkMan sannan ya ɗora sautin AI a kai kafin ya sake yaɗa shi.
Duk da haka, Fadar Shugaban Ƙasa ta fara kiran a gurfanar da VeryDarkMan, inda Bayo Onanuga ya bayyana lamarin a matsayin mummunan hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
Wannan mataki ya jawo suka daga masu binciken gaskiya bayan sun tabbatar da cewa asalin bidiyon VeryDarkMan bai ƙunshi sautin ƙarya da aka yaɗa ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka kama Dennis ba, ko kuma irin tuhume-tuhumen da hukumomi za su gabatar a kansa.
Gwamnatin Tinubu ta nemo mafita kan tsaro
A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamnatin tarayya ta shawarci yan Najeriya da su ba ta hadin kai domin ganin an kawo karshen ta'addanci.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, shi ya ba da wannan shawara inda ya ce gwamnati na kokari kan lamarin.
Ya ce cin nasarar yaƙi da ta’addanci na buƙatar haɗin kan ƙasa baki ɗaya ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini, ƙabila ko yanki ba.
Asali: Legit.ng

