Matasa Sun 'Kona Motar KAROTA a Jihar Kano, An Ji Dalili
- Fusatattun matasa sun ƙona motar aikin hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababaen hawa ta jihar Kano, KAROTA bayan hatsari a Kwanar Dawaki
- KAROTA ta ce matasa sun zargi jami'anta da haddasa wani hatsarin mota wanda ya daga hankalin jama'a, lamarin da ya kai ka kona motar
- Hukumar ta ce jami'anta sun taimaka wajen ceto waɗanda abin ya shafa tare da kai su asibiti yayin da ake kara samun bayanai game da hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu fusatattun matasa sun ƙona wata motar aiki ta Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) bayan wani hatsari da ya faru a yankin Kwanar Dawaki da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun zargi jami'an KAROTA da haddasa hatsarin, lamarin da ya sa suka kai wa jami'an hari tare da banka wa motar aikin hukumar wuta.

Source: Original
Aminiya a kawo labarin cewa Mataimakin Manajan Daraktan KAROTA, Auwal Lawal Aranposu, ya bayyana cewa hatsarin ya shafi wata motar Sharon da kuma wata tirela, inda tirelar ta buge motar Sharon har ta yi ta juyawa sau da dama.
Abin da ya fusata matasa a Kano
Jaridar Punch ta ruwaito a cewar Auwal Lawal Aranposu, lokacin da hatsarin ya faru jami'an KAROTA sun yi ƙoƙarin cafke direban tirelar, amma ya tsere daga wurin.
Aranposu ya ce:
"Nan take wasu da ake zargin ɓata-gari ne suka kai wa jami'anmu hari, saboda suna zaton su ne suka haddasa hatsarin. Daga nan suka ƙona motar aikin hukumar."
Ya musanta zargin cewa jami'an KAROTA ne suka haddasa hatsarin, yana mai cewa aikin da suka yi shi ne ceto waɗanda abin ya shafa tare da kai su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Jama'a sun yi martani a Kano
Wasu daga cikin masu bibiyar shafin sun zargi jamai'an KAROTA da cewa sun yi abubuwan da ba su dace ba a lokacin da hadarin ya afku.
Abdullahi Alh Lungu Gwammaja ya ce:
"Sun yi dai-dai saboda akan gaskiya matansan suke saboda abin da KAROTA sukayi a wurin kuskure ne za'a iya asarar rayuwa kamar yadda suka saba yin sanadin rayuwar al'umma."
Usamah Kabir Alkatsinawee ya wallafa cewa:
"Da alama sun matsa ma mutane shiyasa mutane sukayi masu wannan damyen hukuncin."
An yi magana kan yan sandan jihohi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Kano ta ce 'yan sandan jihohi ba za su kasance da alaka da zabukan 2027 ba kamar yadda wasu ke fargaba ba bayan umarnin shugaban kasa.
Hadimin Gwamna a kan kafafen yada labarai, Ahmed S Aruwa ya tabbatar wa Legit cewa akwai dalilan da suka sa dole aka kirkiri yan sandan jihohi wanda zai taimaka wajen magance rashin tsaro.
Ya bayyana cewa jami'an rundunar jihohi ba za su shafe na tarayya da ake da ita ba wadanda ake ganin cewa su ne za su kula da lamarin, saboda haka zai yi wahala a gansu kan akwatunan zabe.
Asali: Legit.ng

